Saboda rainin wayau daya daga cikin wandanda nake jagoranta limanci a masallaci ya ke buga harka da matata – Lukman a Kotu

Kotun grade one dake Mopo a Ibadan ta warware auren shekara 20 tsakanin wani limami Lukuman Shittu da matarsa Fisayo saboda rashin kauna da zargin zina.
Shittu ya roki kotun da ta raba auren sa saboda zinan da matarsa ke yi na bata masa rai sannan baya kaunar Fisayo a matsayin matarsa kuma.
Ya ce matarsa Fisayo ta canja a lokacin da ya talauce da har bashi da kudin da zai bata domin ta kama shago.
“Fisayo ta yi min karyar wai yan uwanta sun siya mata mota, ashe karyar banza ne, bayan na yi bincike sai na gane cewa ashe wani saurayinta ne da suke buga haraka ya siya mata.
Shittu ya ce tun da ya talauce Fisayo ta rika zuwa gida da dare, ta kwashe ‘ya’yan su uku da suka haifa ta ware da su.
“Fisayo ta canja wa karamin yaron mu makaranta sannan ta sa sauran guda biyu ba za su rika gani na a matsayi mahaifinsu.
“Ya alkali na gano cewa saurayin Fisayo na sallah a masallacin da nake limanci.
Ita kuwa Fisayo ta ce Shittu bashi da mutunci sannan kulun yana yi wa rayuwarta barazana.
Ta ce Shittu ya zuga ni na ciyo bashi daga banki domin in fara sana’a amma sai ya yi amfani da kudin.
“Shittu ya rusa shago na wanda na kama da kudi na domin hana ni kasuwanci.
Alkalin kotun S.M. Akintayo ya raba auren saboda rashin kauna tsakanin ma’auratan.