ZAZZABIN LASSA: Mutum 857 sun kamu da cutar, 164 sun mutu a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa a cikin watanni bakwai daga farkon shekarar 2022 mutum 857 sun kamu da zazzabin Lassa sannan cutar ta yi ajalin mutum 164 a kasar nan.

Hukumar ta ce an gano mutum 857 din da suka kamu da cutar a cikin makonni 29 a fadin kasar nan.

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai sannu a hankali tana ta kama mutanen kasar nan sannan da yawa ana ta mutuwa a sanadiyyar Kamuwa da ita.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

An fara gano wannan cuta a Najeriya a shekaran 1969 a jikin wasu ma’aikatan jinya dake aikin jinkai guda uku a kauyen Lassa a jihar Barno.

Wadannan ma’aikatan jinya dai sun rasu a kauyen sannan cutar ya ci gaba da yaduwa.

A yanzu haka duk shekara sai cutar ta sake bayyana inda mutane da dama ke kamuwa kuma da dama ke rasa rayukansu a dalilin cutar.

Yaduwar cutar

NCDC ta ce a shekaran 2022 cutar ta yadu a kananan hukumomi 99 dake jihohi 24 a kasar nan.

Jami’an lafiya 54 be suka kamu da cutar.

Bisa ga alkaluman yaduwar cutar jihar Ondo na da Kashi 30% na yawan mutanen da suka kamu da cutar, Edo Kashi 26% sannan Bauchi 14%.

Hukumar ta ce a mako na 29 an samu karuwa a yaduwar cutar daga mutum 5 a mako 28 zuwa mutum 10 a mako 29.

An gano wadannan mutane a jihohin Edo da Ondo.

NCDC ta ce duk da haka Najeriya ta samu ragowa a yawan mutanen da suka mutu a dalilin cutar a shekaran 2022.

A shekaran 2021 mutum kashi 23.7% ne suka mutu amma a 2022 mutum kashi 19.1%.

Hukumar ta ce cutar ta fi kama mutane masu shekara 21 zuwa 30 sannan maza sun fi mata kamuwa da cutar.

Rahoton yaduwar cutar da NCDC ta fitar ya nuna cewa a shekaran 2022 an fi samun yawan mutanen da ake zarginsu kamu da cutar fiye da yawan da aka samu a shekaran 2021.

A shekarar 2021 jami’in kiwon lafiya daya ne daga jihar Ondo ya kamu da cutar.