Ƙanjamau ta sake mamaye duniya, bayan sakacin kula da cutar aka maida hankali kan korona -UN

Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna fargabar cewa cutar ƙanjamau ta darkaki duniya baki ɗaya, saboda sakacin da aka yi wajen daƙile ta ciki shekaru uku, aka maida hankali kan korona.

Rahoton UNIAIDS ya nuna cewa yanzu a kowace rana aƙalla mutum 4,000 na kamuwa da ƙanjamau a duniya, lamarin da ya nuna nan da 2025 za a samu ƙarin mutum miliyan 1.2 sun kamu da cutar.

Ci gaban da ake samu wajen daƙile ƙanjamau ya samu koma baya ne saboda kauda kai da aka yi wajen yaƙi da cutar ƙanjamau, aka fi maida hankali wajen daƙile korona.

Haka nan kuma rahoton ya nuna cewa yawan gwaje-gwajen ƙanjamau da kula da masu ɗauke da cutar ya ragu sosai a duniya.

Rahoton na haɗin guiwar UNIAIDS ya nuna damuwar cewa yawan masu bayar da taimakon kuɗaɗe da magunguna ya ragu sosai, mafi yawa ma duk sun janye, in banda Amurka.

Haka da Daraktan Kula da Cutar Ƙanjamau na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana a wurin Taron Duniya kan Ƙanjamau da yanzu haka ke gudana a birnin Montreal na Canada.

Daraktar mai suna Winnie Byanyima, ta ce an fi samun yawan ƙaruwar cutar ƙanjamau a Turai ta Gabas, Tsakiyar Asiya, Latin Amurka da Gabas ta Tsakiya. Sai kuma Afrika ta Yamma.

Sai kuma a kasashen Philippines, Madagascar da Sudan ta Kudu, inda lamarin ya fi muni.

“Masu bayar da tallafi sun ragu da kashi 57% in handa Amurka.”

A halin yanzu dai kashi 43% na masu ɗauke da ƙanjamau su na cikin ƙasashe 52 ne na duniya.

“Waɗanda cutar ta fi saurin kamawa su ne maza ‘yan luwaɗi, karuwai, mazan da ke maida kan su mata da kuma masu ɗirka wa jikin su allurar muggan ƙwayoyi.

“Maza masu luwaɗi da maza sun fi saurin kamuwa sau 28 fiye da sauran fannonin jima’i. Ƙididdigar shekarar 2021 ta nuna cewa a kowane minti ɗaya sai an samu wanda ya kamu da cutar ƙanjamau.”