Dalilai 5 da ya sa ‘ƴan mata su ka fi raja’a wajen murza soyayya da maza masu aure a maimakon samari

Yin soyayya tsakanin mace budurwa da namiji dake da aure ya zama wani abin yi a wannan zamani a dalilin haka PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu ‘yan mata domin gano wasu dalilan da ya sa ‘yan mata suka fi raja’a ga yin soyayya da maza masu aure fiye da samari

Ga dalilan

1. Maza masu aure sun fi kashe wa mace kudi

Amaka Izudomike ta ce ta fi sha’awar yin soyayya da maza masu aure saboda sun fi kashe wa mata kudi.

Ta ce matashi wanda bai da aure ba zai saki jiki ya kashe wa mace kudi Kamar yadda mai aure zai yi ba.
Amaka ta ce matashi zai kashe wa mace kudi idan ya tabbatar za ta aure shi ne ko kuma zai samu wani abu a wurinta.

2. Iya murza soyayya

Pamela Samuel ta ce mazan dake da aure sun fi iya soyayya saboda tun farko sun fito waje daga auren su ne domin neman abinda suka rasa daga wajen matayen su na gida.

3. Karya da saka mata a layi

Asma’u Idris ta ce yin soyayya da namijin dake da aure ya fi mata kwanciyar hankali domin babu cuta ko cutarwa a cikin harkar.

Ta ce da farko namiji mai aure ba zai so ya nuna wa mace cewa yana da aure ba amma idan aka samu daidaituwa kowa ya gane matsayin kowa, shikenan za a yi ta buga harka ce kawai kowa ya san matsayin sa babu damuwa ko muzgunawa.

Idan ko samari ne da ba su da aure, ka dinga fama da karya kenan da talauci da kuma kullum an fita nema.

4. Za a yi soyayya ne cikin Sirri da kama kai babu hayaniya

Nusaiba Sani ta ce maza masu aure sun fi sirri fiye da mazan da basu da aure.

Ta ce namiji mai aure ba zai rika shelan wacce durwa ta bace da ya yi mata sigina za ta gane kawai sai ayi kolabo ba tare da an samu yamutsi ko hayayaga ba. Za a rika murza soyayya cikin kwanciyar hankali, idan ya kai ga ma har aure za a yi, shikenan, idan kuma ba haka ba dama dai babu matsala.

5. Tausayi

Halima Sadauki ta ce maza masu aure sun fi tausayi idan ka manne musu ka nuna musu gaskiyar ka, za ka rika samun abinda kake so cikin kwanciyar hankali ba tare da an fada cikin matsalaba.