Minista Daga Kaduna: ‘Ana so a haɗa ni yamutsi da El-Rufai’ – Korafin Uba Sani ga ƴan jarida

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya gargaɗi ƴan jarida da su rika rubuta sahihan labarai a kafafen su maimakon yayaɗa karerayin da zai iya kawo ruɗani a tsakanin jama’a.
Kakakin fadar gwamnatin Kaduna, Mohammed Shehu a wata sanarwa ranar Asabar ya bayyana cewa gwamnan ya karyata raɗeraɗin da ake yaɗawa wai ya gana da shugaban Kasa Bola Tinubu domin a canja sunan wanda zai maye gurbin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai kujerar minista.
Daya ke zantawa da manema Labarai bayan ganawarsa da shugaba Tinubu, Uba ya ce, ” Duk abin da ake yayaɗawa ba gaskiya bane. Abu kawai dake gaskiya a ciki shine tabbas na gana da shugaban kasa.
” Amma maganan wai canja sunan wanda El-Rufai ya mika don maye gurbin sa ko kuma maganar minista, ban san da shi ma kuma ba mu yi wannan magana da Tinubu ba.
” Abinda kawai yake gaskiya a cikin labarin da ake yayaɗawa shine na gana da shugaban kasa. Duk wani abu karya ne kawai don dai ne a haifar da rikici tsakani na da Malam Nasir El-Rufai. Babu lokacin da muka tattauna batun maye gurbinsu.”
Daga karshe ya yi kira ga ƴan jarida su maida hankali wajen tantance labaran su da kuma tabbatar da fadin gaskiya maimakon watsa abinda ba haka ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin ganawar Tinubu da El-Rufai inda ya janye daga kokarin zama minista a gwamnatin sa.
Majiyoyin mu daga fadar shugaban kasa sun bayyana mana cewa El-Rufai ya shaidawa shugaba Tinubu a ganawa da suka yi a ranar Talata cewa ba ya sha’awar zama minista amma zai ci gaba da ba da gudummawar sa domin ci gaban Najeriya a matsayinsa na dan kasa.
“Ya kuma shaida wa shugaba Tinubu cewa yana bukatar lokaci don mayar da hankali kan karatunsa na samun digirin digir gir a wata jami’a Netherlands.”
Majiya ya shaida wa wannan Jarida cewa tsohon gwamnan ya ba da shawarar a nada wani makusancin sa minista, mai suna Jafaru Ibrahim Sani, yana mai cewa shugaban kasa zai same shimutum da za a yi tafiyar arziki da shi.
Sani ya taba zama kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kaduna (ilimi da muhalli na kananan hukumomi) yayin da El-Rufai ke gwamna.
Mun ji cewa tun bayan ya dawo Najeriya daga Landan, El-Rufai ya nemi ganawa da shugaban kasa, a wannan lokaci ya samu labarin kin tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.
A ganawar, shugaban kasa Tinubu ya snara da El-Rufai cewa ya samu korafe korafe akan sa masu yawan gaske, da yana bukatar rana daya cur domin ya duba su dakyau sannan ya san wani mataki zai dauka.
A daidai wannan lokaci ne El-Rufai ya shaida wa Tinubu cewa, ya hakura da kujerar ministan, tunda kakara na ga ni kuma na ji a jikina akwai wasu zagaye da shugaban Kasa da basu so ya zama minista.
Duk da cewa El-Rufai ya ce, Tinubu ya bashi aikin soma bin diddigin yadda za a gyara harkar wutar lantarki a Najeriya nan da shekara 7, kuma har ya fara aikin gadangadan, sai kuma ga korafi akan sa sannan shugaban kasa bai ce komai a kai ba.