Rashin Mazan aure ya karu a Najeriya saboda tsadar rayuwa, ga kuma mata nan sai lalube suke yi, Daga Mustapha Soron Dinki

Najeriya tana da yawan al-umma. Musamman matasa, matashi shine mutumin da yake tsakanin shekara 15 zuwa 35. Bincike ya nuna cewa, fiye da kaso 70 na ‘yan Najeriya matasa ne. Wad’annan matasa sune kayan aikin cin za6e a karshen kowacce ‘tenure’. Tabbas, dukkan za6unan da aka yi a Najeriya sun tabbatar da haka.

Gaskiyar lamari, da yawa daga cikin matasan Najeriya suna fama da rashin aikin yi. Mafiyawancinsu suna rayuwa ne tsakanin talauci da gwagwarmayar neman sana’a. Wasu kuma suna da sana’ar amma nauyin iyayensu ya dannesu. Rashin tsaro a kasar ya yi sanadin rushewar sana’o’in mutane da yawa.

Aure al’adar d’an Adam ce, har wad’anda ba Musulmai ba. Haka Allah ya tsara rayuwarmu. Wani masanin dabi’ar d’an Adam, mai suna George Peter Murdock yace, ko ina ana yin aure a duniya. Karanta littafin M.K Soron Dinki “The Best Way To Survive In Nigeria”. Karanta “Muqaddima” ta Ibn Khaldun. Tun farkon duniya ana yin aure.

Nema da rayuwar aure suna da alaqa da tattalin arziki. Hakan ne ya sa, tashin farashin abubuwa a Najeriya ya kawo cikas da tasgaro a wajen auren zawarawa da yan mata. Misali, neman aure yana tafiya ne da abubuwa na al’ada, wad’anda su ke cin kud’i. Lefe yana d’aya daga cikinsu, wanda akansa, neman aure da yawa ya lalace. Farashin gidan haya ya tashi, ballantana mallakar gida.

Talauci, tashin kayan masarufi da rashin tsaro sun haifar da mace-macen aure barkatai a gari. Matasa sun koma maula don su rayu. Yan mata da zawarawa sun rasa miji saboda masu auren nasu basu da wadata. Na tattauna da matasa da yawa a garin Kano. Suna son yin auren amma basu da yadda zasu yi. Mutumin da zai iya zama da mace uku, yanzu bai fi karfin zama da mace d’aya ba.

Najeriya tana bukatar taron dangi idan ana neman mafita. Dole sai an ajje adawar siyasa a gefe, an kar6i shawara daga mutanen da su ka cancanta. Mulki ba karamin abu bane, rayuwar al-umma ake tasarifi da ita. Don haka, abun yana bukatar tunani sosai. Shugaba mai inganci, shine wanda yake bude tunaninsa kafin ya aiwatar da abu.

Allah ya shiryar da mu.