Jami’ar Ilori da jam’ar Maiduguri ne jami’o’in Arewa biyu cikin 10 da suka fi dibar ɗalibai a bana

Cikin ɗalibai 551,553 da suka samu shiga jami’o’in Najeriya a 2020, jami’ar Ilori da Maiduguri ne suka fi dibar ɗalibai mafi yawa a shekarar zangon karatu ta 2020.

Ɗalibai 13,634 cikin duka ɗaliban kasar nan da suka samu gurbin karatu a jami’o’in kasar nan ska shiga jami’ar Ilori.

Sai kuma jami’ar Benin dake bi mata.

A 2020, ɗalibai 12,336 suka samu gurbin karatu a jami’ar Benin.

Na ukun su shine jami’ar Maiduguri.

Duk da matsalolin Boko Haram da jihar Barno ke fama da shi, jami’ar Maiduguri ce ta uku wajen baiwa dalibai guraben karatu.

Ɗalibai 11,416 suka samu adimishan a jami’ar.

Kwalejin Kimiya da Fasaha

Kwalejin Kimiya da fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic ne kwalejin da ya fi dibar dalibai a 2020.

Kwalejin ya dibi dalibai 7,740 a 2020. daga shi sai kwalejin Yaba Tch dake Legas, da ya dibi dalibai 3,651

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Legas dalibai 2,461 students; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ilaro Dalibai, 2,422; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ibadan Dalibai , 2,497; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Offa, dalibai 2,249; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Bauchi, 2,372; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Oko, 2,079; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ado-Ekiti, 2,046; Akanu Ibiam, dalibai 2,004.

A kwalejojin Ilimi kuma Kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayya dake Zaria ce ta fi dibar dalibai a wannan shekara, ta dibi dalibai 5,853; Ta Gombe,dalibai 4,179; Ta Kano, Dalibai 4,090; Ta Pankshin, 3,653; Ta gidan waya kuma, 3,567.