RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Shugaban Hukumar Shige da Fice ya yi shigar-burtu, ya kama jami’ai masu cuwa-cuwar yi wa matafiya fasfo a Legas

A ranar Litinin ce Shugaban Riƙon Hukumar Shige-da-fice ta Ƙasa, Isa Idris ya yi ɓad-da-kama ya Ofishin ‘Imagitashin’ na Jihar Legas, a matsayin mai neman a yi masa fasfo. Kuma ya kama wasu jami’an da su ka nemi yin cuwa-cuwar karɓar masa kuɗaɗe kafin su ba shi fasfo ɗin.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da PREMIUM TIMES, Idris ya ce ya tafi shi kaɗai zuwa Ofishin Hukumar na Legas, domin ya tabbatar wa idon sa abin da ake zargin ke faruwa. Kuma shi ma ya ɗanɗana abin da ‘yan Najeriya ke kukan su na ɗanɗanawa a hukumar Shige-da-fice (Nigeria Immigration Services, NIS).

Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa dama shi tun farkon karɓar shugabancin riƙon da ya yi a cikin Satumba, ya sha alwashin magance duk wani ƙalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta kafin a ba su fasfo ɗin fita ƙasashen waje.

Kuma ya sha alwashin ƙarfafa tsaro a kan iyakokin Najeriya tare kuma da inganta walwalar ma’aikatan hukumar baki ɗaya.

Ya ce zuwan da ya yi ofishin Hukumar na Ikoyi da ke Legas a ranar Litinin, ya tabbatar da zarge-zargen da jama’a ke yi a kan jami’an shige-da-fice a Legas a Ikoyi, Ikeja da kuma FESTAC.

Yadda Aka Nemi Yi Min Cuwa-cuwa A Ofishin Ikoyi:

Ya ce ya isa ofishin su na Ikoyi shi kaɗai, kuma babu wanda ya shaida shi. Ya tambayi cewa fasfo ya ke son yi. Sai aka ba shi farashi daban-daban.

“Yayin da na je ofishin Ikoyi, sun damƙa min kwafen takardar da ke ƙunshe da irin fasfo-fasfo ɗin da ake yi. Mai shafi 32 na wa’adin shekaru biyar, su ka ce min Naira 45,000, maimakon Naira 27,000.

“Suka yanka min farashin fasfo mai shafuka 64 ɗan wa’adin shekaru biyar, a kan Naira 55,000, maimakon Naira 37,000.

“Sai kuma fasfo mai shafuka 64 mai wa’adin shekaru 10 a kan Naira 95,000, maimakon Naira 72,000.”

“Daga nan kuma sai su ka tambaye ni ko daga wace jiha na ke. Na ce masu daga jihar Neja. Su ke ce ina da katin ɗan ƙasa, na shaidar haihuwa ta a jihar Neja? Na ce masu ba ni da ko ɗaya. Su ka ce to na biya Naira 3,500 a buga min dukkan takardun da ba ni da su nan take.”

Ya ce har lokacin da ya ke magana da PREMIUM TIMES, jami’an cuwa-cuwar ba su san shi ko wane ne ba. Kuma Kwanturola na Jihar Legas, Bauchi Aliyu ya cika da mamakin ganin sa a ofishin sa a lokacin.

“Ka san shi ma bai daɗe da komawa Legas ba daga Abuja. Bai san na shirya zuwa Legas ba daga Abuja. Har yanzu haka da na ke maganar nan Aliyu cike ya ke da mamaki.” Inji Idris.

Idris ya ce darasin da ya koya zai taimaka wajen tsaftace ayyukan hukumar wajen karɓar fasfo ɗin fita ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa duk ɗan ƙasar da ke riƙe da fasfo ɗin ƙasar sa, kamata ya yi a sake shi mutumin kirki ba mazambaci ba.

“Don haka abin da na gani da ido na, kenan ko ma daga wace ƙasa mutum ya ke, kuma duk irin laifin da ya ke aikatawa ko da ɗan Najeriya ne, idan ya je neman fasfo ɗin fita waje, nan take jami’an mu za su yanka masa farashi ya biya, su buga masa. Ya karɓi abin sa.”

Ya ƙara da cewa nan da makonni biyu zai ƙaddamar da manhajar intanet inda duk mai son sabuntawa ko karɓar sabon fasfo zai riƙa cikewa.

Ya ce zai ƙaddamar da manhajar tare da taimakon Ministan Harkokin Shige-da-fice, Rauf Aregbesola.

Idris ya ce ya zama dole a buɗe manhajar, domin a kawar da yadda ake tururuwa wajen neman fasfo a ofishin hukumar shige-da-fice ɗin.

“Don haka za mu sauƙaƙa hanyoyin riƙa samun fasfo a cikin makonni uku kacal.

“Idan ka ce kai daga Kano ka ke ko kai ɗan Jihar Ribas ne, to tilas sai mun tabbatar, ta hanyar amincewa da al’adun haihuwar ka da sauran takardun shaida.

Jami’an Da Na Kama Da Hannu Dumu-dumu:

Ya ce tuni an rattaba sunayen jami’an da ya kama dumu-dumu da hannu wajen cuwa-cuwar fasfo ɗin, kuma za a hukunta su.