NEMAN DIYYAR NAIRA BILIYAN 4: El-Zakzaky da matar sa sun maka Shugaban SSS da Minista Malami kotu

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zeenah, sun maka Babban Daraktan SSS na Ƙasa da Ministan Shari’a kotu, su na neman diyyar Naira biliyan 4, saboda riƙe masu fasfo da aka yi, aka hana su fita waje neman magani da duba lafiyar su.

A cikin ƙarar da kowanen su ya shigar daban-daban a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, sun sanar da kotu cewa an ƙwace masu fasfo ɗin su tun bayan dawowar su daga Indiya ciki 2019, a tafiyar da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin kai su a yi masu magani, amma abin bai yi nasara ba.

Malamin dai shi da matar sa na zaman shari’ar zargin da Gwamnatin Kaduna ke yi masa na kisa da tara jama’a ba bisa doka ba, shari’ar da aka shafe shekaru a Babbar Kotun Jihar Kaduna.

Kotu ta sallame su, yayin da kotun Kaduna ta ce ba su da wani laifi, a hukuncin da ta yanke cikin watan Yuli, ranar 28.

El-Zakzaky da matar sa sun shaida wa kotu cewa gwamnatin tarayya ce ta yi wa waccan tafiya ta su zuwa Indiya neman magani ƙafar-ungulu.

Bayan da Kotun Kaduna ta sallami El-Zakzaky da matar sa, sai lauyan su Femi Falana ya rubuta wa Hukumar Tsaro ta NIA da SSS da kuma Ofishin Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a, cewa a sakar masu fasfo ɗin su.

Premium Times sun buga labarin NIA ta ce ba ta riƙe da fasfo ɗin El-Zakzaky da matar sa, a cikin wata wasiƙar da su ka aika wa lauyan su Femi Falana.

Falana ya shaida cewa yayin da NIA ta ce ba ta riƙe da fasfo ɗin na su, a cikin amsar da ta maida masa, su kuwa SSS da Ofishin Ministan Shari’a har yau ba su maida masa amsa ba.

Sun shaida wa kotu cewa sun je ofishin Hukumar Shige-da-fice ta Ƙasa, domin neman sanin matsayin da fasfo ɗin na su ke ciki. Sai aka shaida masu cewa akwai umarni daga Hukumar SSS cewa an hana su fita daga Najeriya zuwa wata ƙasa.

Hikimar Shige-da-fice ta sanar da su cewa ba za ta iya sabunta masu fasfo ɗin su ba, har sai bayan an ɗage umarnin hana su fita waje tukunna.

El-Zakzaky da matar sa sun shigar da wannan ƙara a ranar 14 Ga Oktoba. Sun nemi kotu ta kwatar masu fasfo ɗin su, kuma ta haramta riƙe masu fasfo tare da umarnin a ba su damar fita waje neman magani.

El-Zakzaky da matar sa dai su na buƙatar kulawar gaggawa kamar yadda likitar su Ramatu Abubakar ta tabbatar a cikin Satumba, 2021.

Rashin lafiyar su na daɗa yin tsamari sosai, inji rahoton bayanin daga Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.