RAHOTON MUSAMMAN: Yadda ake talauta dubban ‘yan Najeriya a mummunar sana’ar karɓar kuɗin fansar garkuwa da mutane

“Mu ne mu ka yi garkuwa da mijin ki. Sai kun biya fansar Naira miliyan 150 za mu sake shi. Kuma ko kwabo ba za mu rage ba. Saboda mun san mijin ki shi ne shugaban Ma’aikatan Ƙwadago.”

Jin wannan mummunan furuci ya sa matar ta ɓarke da kuka, domin a duniya ba ta taɓa jin irin wannan magana bai ɗaci ba.”

Ba a Jihar Katsina ko Zamfara wannan lamari ya faru ba. A Jihar Cross River ne, inda aka kama Shugaban Ƙungiyar NLC na Jiha, kuma Mista Ukpekpi. Sai bayan wata ɗaya cur su ka kira matar sa, Catherine Ukpakpi, su ka nemi waɗannan maƙudan kuɗaɗen a hannun ta.

Wannan mummunar sana’a ta karaɗe dukkan faɗin ƙasar nan, gabas da yamma, kudu da arewa.

Sai dai kuma za a iya cewa mutanen karkara su ka fi jin jiki. Domin su bayan sayar da gonaki da dabbobi domin biyan kuɗin fansa, har dabbobin na su ake korewa, kuma a ƙone garuruwan su, su gudu yin gudun hijira.

Yayin da idan aka kama babban mutum ake neman fansar miliyan 50 zuwa naira miliyan 100 abin da ya yi sama, ko a kudu ko a Arewa. Idan an kama mai ƙaramin ƙarfi ana tatsar daga Naira miliyan biyu zuwa Naira miliyan 5, ko abin da sauƙaƙa, ko abin da ya yi sama.

Cikin 2017, gogarman mai garkuwa da mutane Chukwudi Evans ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya karɓi dala miliyan 4 a hannun mutum 4, a matsayin kuɗin fansa.

Kuma har yau a kotu ana can ana kwan-gaba-kwan-bayar shari’a, ba a yanke masa hukunci ba.

Garkuwa da mutane ya zama ƙazamar annoba a Arewa, ta yadda ta kai a yanzu haka an karɓi biliyoyin nairori a hannun jama’a da sunan kuɗin fansa a Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Neja da Kebbi.

Kuma yanzu haka wannan mummunar sana’a ita ce babbar barazana a ƙasar nan, har ta kai ga an kulle layukan wayoyin jama’a a wasu sannan jihohin Arewa.

Tsakanin Janairu 2015 zuwa Mayu 2020, aƙalla an yi garkuwa da mutum 4,962 a faɗin ƙasar nan.

Sannan kuma akwai ɗari ruwan garkuwa da ake yi waɗanda kafafen yaɗa labarai ba su ma san an yi ba, ballantana su bada rahoto.

Binciken da SB Morgan Intelligence su ka gudanar tsakanin Yuni 2011 zuwa Maris 2020, sun ce aƙalla an biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane kimanin Naira biliyan 9.

To kuma idan aka yi la’akari daga Maris 2020 zuwa yau tsawon watanni 17 kenan, Allah kaɗai ya san iyakar biliyoyin da ‘yan bindiga su ka karɓe a hannun jama’a da sunan karɓar kuɗin fansa.

Yayin da ake ganin kamar Fulani ne kaɗai ke yin garkuwa da mutane. Su ta su muni ta fi, domin sansanoni gare su a cikin daji. Sannan kuma ga muggan makaman da su ke kai wa garuruwa hari, su na kwasar jama’a da ɗaruruwan ɗalibai.

Amma bincike ya nuna kusan kowace ƙabila akwai masu garkuwa da mutane.

A Arewa inda matsalar ta fi muni, akwai ɗaruruwan mutane yanzu haka s cikin daji s hannun ‘yan bindiga, waɗanda sai an kai kuɗin fansa kafin a sake su.

Garkuwa da mutane ya kassara Arewa ta ɓangaren tattalin arziki. Yayin da yawancin mutanen karkara su ka daina zuwa gonakin su, wasu da dama sun sayar da gonakin sun biya kuɗin fansar kan su, ko fansar ‘yan’uwan su.