Boko Haram ta fara horar da matasa a wasu garuruwan jihar Neja

Rahotanni na cewa mayakan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a jihar Neja, inda suke bai wa mazauna ƙauyuka kuɗi tare da sanya su cikin jerin manyan mayakansu.

BBC ta ruwaito Shaidu sun ce ‘yan tada kayar bayan galibinsu dauke da manyan bindigogi sun bulla a wasu kauyukan da ke karamar hukumar Shiroro inda suke yiwa mutane wa’azi, al’amarin da ya jefa jama’a cikin fargaba da tashin hankali.

Bayanan da BBC ta tattaro daga wasu yankuna na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja na cewa, ‘yan Boko Haram din sun karbe garuruwa masu dumbin yawa.

Wani shaida da ya gudu zuwa birnin Minna daga garin Kurebe saboda fargaba, ya shaida mana ta waya cewa, ‘yan Boko Haram suna tara mutane suna yi musu wa’azi.

  • Boko Haram ta fara horar da matasa a wasu garuruwan jihar Neja
  • Wanda ya yi zanen batanci akan Annabi ya mutu

Baya ga Kurebe, ‘yan Boko Haram din sun kuma bulla a makwaftan garuruwa ciki har da Mashekari da Lukafe da Kusaka da Sabon Gida da kuma Kwaki Chukuba.

Wani mutumin yankin yace har sun fara yiwa mutane hukunci.

BBC ta yi kokarin tuntubar kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris, amma hakata ba ta cimma ruwa ba.

Sai dai rahotan da kamfanin dillancin labarai na Reuter ya yi, ya ambato kwamishinan yana tabbatar da bullar mayakan na Boko Haram a wasu yankuna na karamar Hukumar Shiroro.

Haka kuma, Alhaji Sani ya fadawa Reuters din cewa gwamnatin jihar da kuma jami’an tsaro sun dukufa don dakile bazuwar ‘yan Boko Haram din zuwa wasu yankuna.

A baya-bayan dai kusan ‘yan Boko Haram dubu takwas ne suka miƙa wuya ga hukumomin Najeriya.

Sai dai bullar mayakan ‘yan tada-kayar-bayan a jihar Neja da ke kusa da babban birnin Najeriya Abuja, wani al’amari ne da ke sake fito da bukatar yin hubbasa don kakkebe duk wata barazana da birnin ka iya fuskanta.

An wallafa wannan Labari October 4, 2021 11:27 PM