RAHOTON MUSAMMAN: Duk da ɗimbin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a fannin noma, har yau an kasa noma wadataccen rogo a Najeriya

Garin rogo, wanda a ƙasar Hausa aka fi sani da garin kwaki, ya na ɗaya daga cikin abincin da duk wanda a shekarun baya aka ga ya daddage ya na ƙasumar sa, to ana danganta shi da talauci ko ƙarancin wadatar aljihu ko ta abinci a gida.

Amma a yau, duk da ɗimbin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen bunƙasa noma, hakan bai hana garin kwaki fecewa a guje ba, ya bi sahun sauran kayan abincin da ake nomawa a gida wajen tsula tsadar tsiya.

Kamar yadda shinkafa, wake, masara, gero da dawa su ke neman su gagari talaka, tuni shi garin rogo ya shige gaban su wajen tsada. Ya tsere wa gero da dawa da masara. Kuma ya yi wa talaka fintinkau, sai gani sai hange daga nesa.

Buhun garin kwaki mai nauyin kilo 100, wanda a shekarun baya ake sayarwa naira 16,000, yanzu idan ba ka da naira 40,000 ba za ta ka iya sayen sa ba a jihohi irin su Cross River, inda ake ganin kamar can ne ma ya fi arha takyaf.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna dalilai da dama da su ka haddasa ko da talaka ya iya sayen garin kwaki domin ya ci, to ba zai iya yi masa cin a ci a ƙoshi ba, irin wanda a shekarun baya ake tasa taiba a gaba ana ci har ciki ya cika.

Miliyoyin ma’aikatan da su ka ƙunshi na gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi waɗanda albashin su bai kai naira 40,000 ba, ba su iya cin garin kwaki su ƙoshi su da iyalan su. Sai dai a yi cin daga-bana-sai-baɗi, wanda ake yi ranar da aka ɗauki albashi.

Maciya tuwon alabo, wanda ake yi da rogo, su ma yanzu sai gani sai hange, ba kowa ke iya buɗe ciki ya danƙari tuwon alabo ba, duk kuwa da sulɓin ta lomar tuwon ke da shi. Saboda ba ta da sulɓi a cikin aljihun talaka.

A Najeriya dai batun tsadar abinci kullum sai hauhawa ya ke yi, ya ƙi saukowa ko gsngarowa ko kuma mirginowa a ƙasa.

A ƙididdigar da Hukumar Ƙididigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa ta yi a watan Afrilu, ta nuna cewa cikin watan Maris, 2021 kayan abinci a Najeriya sun yi tsadar da ba su taɓa yi a tsawon shekaru huɗu da su ka gabata ba.

Garin kwaki wanda shi ne aka fi nomawa na biyu daga masara a ƙasar nan, a yanzu bincike ya nuna wanda ake nomawa ɗin ba ya wadata.

Manoma irin su Grace Ebit da wasu masana sun danganta matsalar da rashin nahartaccen tsari da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, rashin kyakkyawan tsarin noma, rashin jari ko rashin lamuni daga gwamnati da kuma ƙarancin taki.

Masana sun ce kafin rogo ya sake yin arha a Najeriya, sai an dasa aƙalla metrik tan miliyan 28.3 a filin gonakin da aƙalla sun kai faɗin hekta miliyan 1.2.

Sai dai Hausawa sun ce kowa ya tuna Bara ai bai ji daɗin bana ba. Grace cewa ta yi:

“Albarkar ƙasar noma a yanzu ba ta kai ta shekarun da su ka gabata ba. Sannan kuma ga matsala gagarima ta tsaro. Manoma da dama na tsaron zuwa gona, kada manomi ya je a yi garkuwa da shi, a ƙarshe a sayar da gonar da ya ke taƙama a bisa kudin fanso shi.”

Duk da nasarori da matsalolin da Najeriya ta riƙa samu wajen noma tsawon shekaru masu yawa, har yau an kasa noma wadatacce rogon da zai wadaci ƙasar nan, mai al’umma miliyoyin da ke sarrafa rogo ana abinci da sauran sinadaran masarufi masu yawa da shi.

Matsalolin da su ka haddasa rashin noma wadataccen rogo a Najeriya su na da yawa. Akwai rashin kyakkyawan tsari daga gwamnati. Sai kuma rashin kyakkyawan tsarin noman shi kan sa da kuma rashin bayar da isasshen lamuni ga manoma rogo. Akwai kuma rashin wadataccen takin zamani.

Yayin da ake buƙatar metrik tan 300,000 na rogo, wanda ake iya nomawa a Najeriya bai wuce metrik tan 10,000 kacal ba. Watau ana neman cikon metrik tan 290,000 kenan, kamar yadda PricewaterhouseCoopers su ka bayyana, a cikin rahoton su na watan Disamba, 2020.