Masu garkuwa sun bullo da wata sabuwar hanyar karban kuɗin fansa

Masu satar mutane a babban birnin Tarayya Abuja sun fara tabbatar da rashin tsoron matakan da gwamnati ke ɗauka na tsato, infa suke gudanar da ta’asar su kai tsaye, a halin yanzu sun fara karbar kuɗin fansa ta asusun banki.

A makon da ya gabata dakaɗai ƴan bindigar su yi kai hari sau biyu a unguwar Tungan Maje, dake wajen birnin Tarayya Abuja. Maharan sun sake komawa unguwar a aranar Laraba, bayan da sun sace mutane 6 a baya.
Sauran garuruwan kewaye da Abuja kamar su Kuje, Bwari, Abaji sun fuskanci tsanantar ayyukan masu satar mutane a ‘yan watannin da suka gabata kamar yadda majiyarmu ta RFI ta ruwaito.
A yayin da waɗannan masu satar mutane kan saki wadanda suka kama bayan an biya kuɗin fansa a hannu, yanzu wani sabon salo suka bullo da shi na karbar kuɗin fansa ta asusun banki.
A watan Afrilun da ya gabata, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Kingsley Mogalu ya yi zargin cewa masu satar mutane da ƴan ta’adda sun fara neman a biya su da kuɗin intranet na cryptocurrency, inda ya nemi hukuma ta bullo da matakan daƙile su.
Wasu iyalai sun bayyana yadda masu satar mutane suka tilasta musu biyan kuɗin fansa ta banki, bayan da suka sace musu ƴan uwa a garin Madalla dake ƙaramar hukumar Suleja.
Mista Adewuyi, da aka yi garkuwa da matarsa ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa ƴan bindigar sun umurce shi ya biya kuɗin fansar maiɗakinsa ta asusun bankin Access mai lamba: 1403762272 da suna: Badawi Abba. Adewuyi ya ce ya kai rahoton al’amarin ga ofishin ‘yan sanda dake Jabi Abuja.