An roƙi Bankin CBN ya rataya wa naira layar laƙanin hana ta firgita idan ta yi ido-biyu da dala a kasuwannin hada-hada

Wani masanin ƙabali da ba’adin harkokin kuɗaɗe, Okechukwu Unegbu, ya roƙi Babban Bankin Najeriya (CBN) ya lalubo hanyoyin da zai saisaita tsadar kayan abincin da kayan masarufi ta hanyar dakatar da yawan farfaɗiya da faɗuwar ‘yan bori da naira ke yi a kasuwannin hada-hada na ciki da wajen ƙasar nan.

Okechukwu ya ce tsadar kayayyaki na ƙara tsananta cikin ƙasa, saboda darajar naira na ci gaba da taɓarɓarewa, sannan kuma a waje ko cikin gida duk inda naira ta yi ido-biyu da dala, sai ta fara karkarwa ta na firgita.

Okechukwu wanda shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Mashahuran Masana Harkokin Kuɗaɗe na Cibiyar CIBN ta Najeriya, ya bada wannan shawara ce a ranar Lahadi, a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Ya ƙara da cewa yawan karyewar darajar naira da ake fuskanta abin damuwa ne, domin yanzu akwai wasu sinadarai da su ka kamata a yi amfani da su, wajen ƙara wa naira ƙarfi ta daina yawan firgita ko faduwar-‘yan-bori.

“Ya kamata Kwamitin Tsare-tsaren Ka’idojin Hada-hadar Kuɗaɗe na CBN ya yi nazarin shingayen da za a gindaya wa naira, matsayin kan iyakar da za a hana ta tsallakewa, kamar yadda bankin ya yi sau shida a baya.

“Har yanzu tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki na hauhawa a Najeriya. Ƙuɗaɗen ruwan da bankuna ke bayarwa kuma sai hawa-da-sauka su ke yi. Sannan kasuwar canjin kuɗaɗen waje kuwa a nan ne aka fi yi wa naira laga-laga ko da kallo ta je, ballantana ta je cin kasuwar.

“Yanzu kusan naira 500 ce daidai da dala 1. A Najeriya idan ka na da naira 500, za ka iya cin abinci garau-garau har a jefa maka ‘yar tsokar nama. To inda tsiyar ta ke, idan ka je Amurka a can dala 1 babu abin da za ta yi maka.”

A ƙarshe ya bada shawarar cewa a yanzu da farashin ɗanyen mai ya yi sama a kasuwar duniya, ya kamata Kwamitin MPC na Bankin CBN ya bijiro da tsarin da zai samar da ayyukan yi sosai a ƙasar nan.