RAHOTO: Duk da maƙudan biliyoyin nairorin da Buhari ke narkawa a fannin noma, gwamnatin sa ce koma-baya a noma tun daga 1999 zuwa yau

Lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Ƙasa a 2015, ya yi alƙawarin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta hanyar rage dogaro da ɗanyen man ferur.

Ya ce zai maida hankali wajen bunƙasa noma domin wadata ƙasa da abincin da za ta daina dogaro da abincin da ake shigowa da shi daga waje.

Buhari ya ce zai inganta noma yadda shi ma zai zama hanyar fitar da kayan abinci ana samun kuɗaɗen shiga daga waje.

Buhari ya ƙaddamar da Shirin Bunƙasa Noma (APP), wanda wa’adin shirin ya cika a cikin Disamba, 2020. Wannan shiri na ya maye gurbin shirin Ajandar Bunƙasa Noma (ATA), wanda Goodluck Jonathan ya ƙaddamar.

An tsara shirin APP bisa tsare-tsare daban-daban manya da ƙanana domin a bunƙasa harkokin noma.

2015-2021: Yanzu dai an cika shekaru shida kenan da hawan Buhari kan mulki, kuma shekaru shida da yin wacan alƙawari na bunƙasa harkokin noma. Sannan kuma saura shekaru biyu kenan wa’adin shekaru takwas na Buhari.

Kididdigaggun bayanai sun tabbatar cewa duk da maƙudan kuɗaɗen da Buhari ya riƙa narkawa a fannin noma fiye da gwamnatocin baya, waɗancan gwamnatoci na daga 1999 har zuwa yau, sun fi Gwamnatin Buhari tabuka abin a-zo-a-gani a fannin noma.

Dandalin Ƙididdigar Alƙaluma mai suna Statisense, ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar na mulkin Buhari, harkokin noma sun bunƙasa da kashi 15% kacal.

“Amma harkokin noma sun bunƙasa da kashi 133% a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, kashi 19.1% a taƙaitaccen lokacin Umaru ‘Yar’Adua, sai kuma kashi 22.2% a zamanin Goodluck Jonathan.”

Sai dai kuma binciken da Cibiyar Binciken Ƙwaƙwaf ta PREMIUM TIMES (PTCIJ) ta gudanar, ta binciko cewa Gwamnatin Buhari ta yi amfani da noma wajen bunƙasa tattalin arzikin cikin ƙasa (GDP), fiye da gwamnatin Jonarhan kaɗai.

Bayanan da su ka faɗo hannun PTCIJ sun tabbatar cewa Gwamnatin Obasanjo ta bunƙasa tattalin arzikin cikan sa ta fannin noma da kashi 27.5%, sai kuma kashi 25.6% a zamanin gwamnatin ‘Yar’Adua. Kashi 21.75 a zamanin Jonathan, sai zamanin Buhari.

Steve Okeleji, Shugaban AHAN ya ce akwai tsare-tsaren bunƙasa harkokin noma, amma aiwatar da tsare-tsaren shi ne matsala, kuma can ake samun cikas.

Ya ce akwai buƙatar saka manoma ko masana harkokin noma waɗanda ba jami’an gwamnati ba a cikin tsare-tsaren bunƙasa noma.

Tsakanin Kuɗaɗen Basussukan Manoma Da Albarkar Noma: A Ina Matsalar Ta Ke?

Gwamnatin Buhari ta riƙa kamfatar maƙudan kuɗaɗe ta na bayarwa da sunan ramce ga manoma a ƙarƙashin Shirin ‘Anchor Borrowers’, da nufin bunƙasa noman kayan abincin da aka hana shigowa da su, musamman shinkafa.

Sai dai wannan bai hana dukkan kayan abincin da ake nomawa a Najeriya tsula tsadar tsiya har su ke neman gagarar talaka ba.

Gero, dawa, shinkafa, wake da sauran kayan gonar da Buhari ya riƙa raba wa manoma bashi don su noma, duk sun nunka farashin su na da kafin Buhari ya hau mulki, maimakon a ramu rangwame sosai fiye da farashin gwamnatocin baya.

Yayin da gwamnatin Buhari ke tutiya da bunƙasa noma, a lokacin ne kuma amfanin gonar da ake nomawa a cikin gida ya fi tsada.

Sannan kuma matsalar tsaron da ke neman ta gagari gwamnatin Buhari daƙilewa, ta ƙara maida harkar noma baya, saboda manoma da dama sun tsere daga gonakin su. An kashe wasu, wasu da dama an lalata masu amfanin gona, an kwashe na kwashewa, wasu kuma masu garkuwa su damƙe su, sun sayar da gonakin da amfanin gonar sun biya kuɗin fansa.