Kada ƴan Najeriya su tada hankali, za mu san yadda za su ci gaba da mu’amula da Tiwita – Sakon Tiwita ga ƴan Najeriya

Kamfanin Tiwita da ke yanar gizo ya bayyana cewa kada ƴwn Najeriya su wani damu da dakatar da dandalin daga aiki a Najeriya, cewa za su tabbatar mutanen Najeriya sun ci gaba da harkokin su a dandalin duk da dokar da Najeriya ta saka.

” Abinda gwamnatin Najeriya ta yi ya saɓa da dama da mutane ke dashi na watayawa da sanin duk abinda suke so na kafafen sada zumunta na zamani. Zamu tabbatar ƴan Najeriya ba su gagara shiga shafin mu ba”.

Sai dai tun da farkon yinin Asabar Ministan Shari’a Abubakar Malami ya gargadi ƴan Najeriya da kakkausar murya cewa duk wanda ya karya dokar dakatar da tiwita da Najeriya ta yi, zai fuskanci hukuma.

Malami ya ce an saka doka a kasa kuma doka ce abi doka, saboda haka idan wani ya ci gaba da amfani ko aiki da dandalin Tiwita, zai fuskanci tuhuma daga gwamnatin Najeriya.

Ministan ya umarci hukumomin da abin ya shafa su tabbata sun bi avun sauda kafa domin tabbatar da babu wanda ya karya dokar daina amfani da Tiwita a kasar nan.

Dakatar da Tiwita a Najeriya

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, Olumide Akpata, ya kalubalanci gwamnatin Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta gaggauta janye dakatar da Tiwita da ta yi ko su hadu da ita a kotu.

Idan ba a manta ba Kungiyar SERAP ce ta fara bayyana rashin jin dadin kan dakatar da Tiwita da gwamnatin tarayya ta yi ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya din haramtacce ne,