Rahotanni sun ce Sojojin Najeriya sun kashe gogarma Kachalla da Auta a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa Sojojin Najeriya sun kai hari a sansanin manyan ‘yan bindiga da ke Zamfara, inda su ka yi nasarar kashe babban gogarma Kachalla Ruga da Alhaji Auta.

Jaridar PR Nigeria ta ruwaito cewa sojoji sun kashe Kachalla da Auta ne a ranar sabuwar shekara ta 2022 a cikin dajin Zamfara.

Sai dai kuma wannan jarida ta kasa samun Kakakin Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, Benjamin Sawyer, domin ya tabbatar da sahihancin rahoton.

PR Nigeria, wadda jarida ce mai kusanci da sojojin Najeriya, ta ruwaito cewa an kashe kwamandojin ‘yan bindiga ɗin ne yayin da Sojojin Saman Najeriya a ƙarƙashin ‘Operation Hadarin Daji” suka jefa masu bama-bamai.

An jefa masu bama-bamai ɗin ne bayan sojoji sun samu kwarmaton inda maɓuyar maharan ta ke a cikin Dajin Gusami da ƙauyen Tsamre a cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara.

An kai masu harin ne da jijjifin safiyar Asabar ta ranar farko ɗin sabuwar shekara ta 2021.

Rahoton ya ƙara da cewa, “wasu ‘yan bindiga da suka taru a gidan Auta domin yi masa jana’iza, an jefa masu makami mai linzami daga kan wani jirgin yaƙi, inda aka kashe wasu da dama waɗanda ba a tantance yawan su ba.” Inji rahoton.

“Harin da sojojin sama su ka riƙa bin masu ƙoƙarin tserewa ma ya yi sanadiyyar karkashe su da yawa, duk kuwa da cewa su na gudu su na boyewa ƙarƙashin bishiyoyi.”

“Har zuwa yanzu dai ba a san inda wasu kwamandojin ‘yan bindiga irin su Alhaji Nashama, Shingi da Halilu su ke ba. Ana ganin ko dai ko an raunata su sun gurgunce, ko kuma sun arce.” Haka rahoton ya bayyana.

Benjamin Sawyer wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, bai ɗauki wayar kiran da aka yi masa ba. Kuma bai maida wa wakilin mu amsar saƙon tes ɗin da ya tura masa ba, domin ya tabbatar masa da faduwar hakan.