ZAƁEN ƘANANAN HUKUMOMIN ABUJA: INEC ta yi wa ƙungiyoyin sa ido 51 rajista

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa wasu ƙungiyoyi su 51 rajista domin su sa ido kan zaɓen da za ta shirya a ƙananan hukumomin da ke Gundumar Birnin Tarayya (FCT) a ranar 12 ga Fabrairu, 2022.

A wata sanarwa da hukumar ta bayar a ranar Laraba a Abuja, ta bayyana cewa jerin sunayen ƙungiyoyi da ta amince da su ɗin sun haɗa da ƙungiyoyi 50 ‘yan ƙasa da kuma guda ɗaya daga ƙasar waje.

A cewar sanarwar, ƙungiyoyin ‘yan ƙasa da aka yi wa rajista sun haɗa da ‘Advocacy for Quality Leadership and Health Awareness Foundation’, ‘Africa for Millenium Change Initiative’, da ‘Centre for Democracy and Development’.

Akwai kuma ƙungiyar lauyoyi ta ‘Nigeria Bar Association’ da ‘Nigeria Civil Society Situation Room (Policy and Legal Advocacy Centre)’, yayin da ƙungiyar ‘yan ƙasar waje da aka yi wa rajista ita ce ‘International Foundation for Electoral Systems’.

Hukumar ta shawarci ƙungiyoyin da aka yi wa rajistar da su cike duk wasu takardu da ake buƙata ta hanyar yanar gizo a wannan gidan yanar: (http://observergroups.inecnigeria.org/) daga ranar 29 ga Disamba, 2021 zuwa ranar 13 ga Janairu, 2022.

Haka kuma hukumar ta nanata buƙatar da ke akwai ta ‘yan sa idon su kiyaye dukkan sharuɗɗan kare kai daga kamuwa da cutar korona (COVID–19) waɗanda INEC ta fito da su kan harkar zaɓe da kuma yi wa ‘yan sa ido rajista.

Wannan, inji INEC, ya haɗa da rattaba hannu kan wani fom na sahale wa hukumar da kuma bayar da kayan aiki na kare kai da ake kira ‘Personal Protective Equipment’ (PPE) ga dukkan masu aikin sa ido.

Ta yi gargaɗin cewa “duk wanda ya kasa bin sharuɗɗan za a soke rajistar sa ba tare da ɓata lokaci ba.”

INEC ta ce rarraba kayan aiki ga masu aikin sa ido ‘yan ƙasa (da su ka haɗa da katin shaida ga kowane mai sa ido) za a yi shi ne a ofishin ta da ke Abuja daga ranar 3 ga Fabrairu zuwa ranar 11 ga Fabrairu, 2022.