BANKWANA DA 2021: Shekarar da Majalisar Dattawa ta yi zama sau 66, maimakon sau 181 da doka ta tanadar

Majalisar Dattawa, inda can ne ake kafa dokokin da ke cikin Kundin Mulkin Najeriya, ta kasance ita ce a sahun gaba wajen karya dokokin Najeriya a shekarar 2021.

Tsarin Mulkin Najeriya ya gindaya cewa wajibin Majalisar Dattawa ne ta yi zama na aƙalla sau 181 a kowace shekara, wato zaman kwana 181 a cikin kwanaki 365.

Maimakon haka, dattawan ba su dubi darajar dokokin da su ke kafawa ba, kuma ba su daratta gemun su ba wajen bin ƙa’ida. Sai su ka yi zama sau 66 kacal a cikin kwanaki 365 na shekarar 2021.

Sannan kuma dattawan sun karya ƙa’idar da Majalisa ta gindiya, inda “Umarni na 13(2) ya ce su rika zama a ranakun Talata, Laraba da Alhamis a kowane mako.”

Majalisar Dattawa ta karya wannan umarni, inda a cikin 2021 ta riƙa zama a ranakun Talata da Laraba kawai.

Hakan na nufin Majalisar Dattawa ta yi zaman watanni biyu da kwanaki shida kaɗai, maimakon zaman yawan kwanakin watanni shida cur.

PREMIUM TIMES ta binciko cewa Majalisar Dattawa ta tafi hutu har sau takwas a cikin 2021. Kuma hutun kan kama daga mako ɗaya har zuwa makonni huɗu.

Tsakanin 34 Ga Fabrairu, zuwa 22 Ga Disamba, Majalisa ta je hutu sau takwas.

Hutun kan kasance ko dai na tafiya zaman makokin wani ɗan majalisa da ya mutu, hutun Sallah ko na Kirsimeti, ko kuma hutun tafiya duba-garin ayyuka a matsayin su na kwamitin ɓangarori daban-daban.

Hutun farko da su ka fara tafiya a cikin 2021, shi ne hutun da aka bayar domin Sanatocin APC su je su yi sabunta rajista tare da tantance ‘yan jam’iyya.

A farkon 2021 dai kamata ya yi a ce sun koma aiki a ranar 23 Ga Janairu, 2021. Amma sai aka ƙara hutun zuwa 9 Ga Fabrairu, domin ‘yan APC su samu damar zuwa sabunta rajistar jam’iyya. Daga nan kuma sai da su ka ƙara tafiya wani hutun har sau bakwai a cikin 2021.

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa kamata ya yi a daina kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen tafiyar da majalisa. Su na ganin a rage yawan su, kuma kowa ya zauna a jihar sa, sai ranar zaman majalisa ya je ya halarta.