QATAR 2022: An haramta wa ‘yan kallo shan kowace irin taba sigari a cikin sitadiyan

Hukumar Lafiya ta Duniya tare da haɗin kan Gwamnatin Qatar sun haramta sha, sayarwa ko tallata kowace irin taba sigari a sitadiyan yayin wasannin cin kofin ƙwallon duniya da za a fara a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da WHO ta fitar a ranar Alhamis kuma ta aiko wa PREMIUM TIMES, ta ce an gindaya waɗannan matakai da ƙa’idoji ne domin a tabbatar wasanni sun zama dandalin inganta lafiyar jama’a da kuma kare su daga kamuwa da cututtuka.

Wannan haɗin gwiwa tsakanin WHO da Gwamantin Qatar wanda aka fara tun cikin Oktoba 2021, ya samu cikakken goyon bayan Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), a matsayin wasu matakan shelanta inganta lafiya ta hanyar ƙwallon ƙafa.

Ministan Harkokin Lafiya na Qatar, Hanan Al Kuwari ne ya bayyana cewa FIFA Qatar 2022 zai kasance wuri ne na yi wa duniya shelar hanyoyin inganta lafiya baki ɗaya.

Al Kuwari ta ce wasanni ba su yiwuwa sai da cikakkiyar lafiya. Kuma sai da lafiya ake murnar wasanni da annashuwa.

“Haɗin guiwa tsakanin Wasanni da Lafiya abu biyu ne. Na farko a bunƙasa wasanni ni. Na biyu kuma a yi ƙoƙarin inganta lafiya da kuma kare al’umma daga kamuwa da cututtuka.

Don haka ta ce an haramta shan kowace irin nau’in taba sigari ko sayar da ita da tallata ta a dukkan sitadiyan ɗin da za a yi wasannin ƙwallon duniya a ƙasar.

Qatar ta haramta wa ‘yan kallo shan kowace irin taba sigari a cikin sitadiyan.