Dalilin da ya sa jami’ar Maryam Abacha ta sakawa ginin sashen Koyon Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa sunan Atiku Abubakar – Farfesa Gwarzo

Fitacciyar Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano ta saka wa ginin sashen Koyon Zamantakewa da Gudanarwa na jami’ar sunan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Atiku, wanda ya kaddamar da ginin a ranar Laraba, 31 ga watan Agusta, 2022, ya samu rakiyar jiga-jiga-jigan jam’iyyar PDP a ziyarar da ya kai jami’ar da ke Hotoro GRA, Kano.
Shugaban jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa jami’ar ta yi haka ne don jinjina gudunmawar da Atiku ya baiwa ilimi a kasar nan.
” Ni ba ɗan siyasa bane, mun karrama Atiku saboda irin gudunmawar da ya baiwa ilimi a kasar nan ne musamman a fannin jami’o’i masu zaman kansu. Haka kuma babu wani shakuwa tsakani na da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal amma kuma MAAUN ta karrama shi da digirin digirgir.
” Kafa jam’iyyar ABTI, ya kara mana kwarin guiwar kafa jami’ar MAAUN,
Farfesa Gwarzo ya kara da cewa tun farko ya kafa jami’ar MAAUN a Nijar ne domin samar da mata da suka kware a harkar ilimin kiwon lafiya da ake ƙarancin su a musamman yankin Arewa.
A nashi jawabin, ɗan takarar shugaban Kasa Atiku Abubakar ya jinjina wa Farfesa Gwarzo bisa wannan babban himma da yayi na kafa jami’a dake koyar wa dadidai da yadda jami’o’in Amurka ke yi sannan kuma da Karrama shi da jami’ar ta yi.