PDP ba gadon gidan ku bane – Martanin Obaseki ga Wike

Gwamnan jihar Edo ya maida wa gwamnan Ribas Nyesome Wike martani inda ya gard’gaɗeshi da ya daina yi wa jam’iyyar bababkere ya na yi kamar PDP gadon gidan su ne babu wanda ya isa da jam’iyyar.

Obaseki ya ce mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu bai yi barazanar ficewa daga jam’iyyar ba kamar yadda Wike ya ce, shi Wiken ne yake yi wa jam’iyyar barazana akai akai.

” In banda zautuwa da nuna isa mutum shi kadai kullum sai ya rika nuna babu wanda ya isa da shi a jam’iyyar PDP, kamar gadon gidan su.

” Dukkan mu ƴaƴan jam’iyyar ne kuma kowannen mu na da iko akan jam’iyyar kamar kowa. Saboda haka ya daina huhhura hanshi yana yi wa mutane babakere kamar shine kaɗai wanda ya isa akan jam’iyyar.

Obaseki ya zargi Wike da mataimakin Jam’iyyar na yankin kudu Maso Kudu Dan Orbih da yi kutunguilar kawo ruɗani a jihar.

” Ina son Wike da ƴan koron sa su sani cewa ba za su iya rusa jam’iyyar ko kuma kawo ruɗani a cikin ta ba kamar yadda yayi a jihar Cross Ribas saboda neman jam’iyyar ta tsaida shi takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Kalaman da mataimakin gwamnan jihar Edo babu ruɗani a cikin sa. Yayi magana ne a matsayin shi na matashi domin matasan Najeriya. Idan Wike ba zai iya sauraren korafin matasa ba, yaya zai yi da su a vurin sa na zama shugaban kasa da yake da shi.

Wike ya ce idan ba a hukuntashi ba bisa kalaman da yayi, zai yi amfani da karfin Idon da yake da shi ya hukunta shi da karfin tsiya ko jam’iyya ta so ko bata so ba.