HARƘALLAR HUSHPUPPI: ‘Ni ban wanke Abba Kyari daga zargin damfarar dala miliyan 1.1 ba’ -Minista Malami

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ƙaryata wani rahoto da aka buga cewa ya na ƙoƙarin wanke Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari daga zargin damfarar da ƙasar Amurka ke yi masa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Minista Malami mai suna Abubakar Gwandu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce rahoton da jaridar Punch ta buga ba gaskiya ba ne.

Punch ta buga labarin cewa Malami na shirya wata sabuwar gada, wadda Abba Kyari zai bi ya tsallake siraɗin tuhumar da mahukuntan Amurka ke yi masa.

Sai dai kuma a raddin da Malami ya mayar, ya ce ba wata sabuwar gada ya ke shiryawa ba, ya dai shawarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ne cewa su ƙara zurfafa binciken yadda Abba Kyari ya haɗa baki da Hushpuppi sosai, ta yadda za a samu ƙwararan hujjoji.

Punch ta ruwaito cewa Malami ya shaida wa ‘yan sanda cewa babu hujjojin da za su nuna Kyari ya yi laifi.

Sai dai kuma sanarwar ta ce Punch da ma sauran kafafen da suka buga rahoton na Punch, ba su fahimci Minista Malami ba.

“Ministan Shari’a Abubakar Malami cewa ya yi har yanzu ba a kai ƙarshen kammala binciken gama tattara hujjoji ba. Saboda haka rundunar ‘yan sanda ta ƙara zurfafa binciken ta, ta yadda za ta ƙara wa daɓen hujjojin da ta ke da su makuba sosai.”

Bayan an dakatar da Abba Kyari tun cikin watan Yunin 2021, cikin Fabrairu 2022 kuma sai jami’an Hukumar NDLEA su ka damƙe shi, bayan sun zarge shi da laifin harƙallar shigo da hodar Ibilis daga Brazil da Habasha.

Bayan an gurfanar da shi da sauran mutum shida da ake zargin su, tun a ranar farko ta sauraren shari’ar dai dillalan shigo da ƙwayar su biyu, su ka amsa laifin su.

Amma Kyari da sauran ‘yan sanda huɗu ba su amsa laifin su ba.