NOMAN RANI: Gwamnatin Tarayya ta damƙa wa manoman Jigawa hekta 289

Gwamnatin Tarayya ta maida wa manoman Jigawa hekta 289 na gonakin noman rani a ƙarƙashin Shirin Gari Irrigation Project.

Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Harkokin Samar da Ruwa, Kenechukwu Offie ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Ministan Harkokin Noma, Suleiman Adamu ne ya damƙa masu filayen a ranar Juma’a, bayan kammala wani aikin noman rani da aka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa aƙalla manoma 1,472 ne za su amfana da shirin.

Shirin ya na a ƙarƙashin ƙudirin Shugaba Muhammadu Buhari na ganin an haɓaka tattalin arziki, wadatar abinci da kuma inganta walwalar ‘yan Najeriya.

Ya na a ƙarƙashin shirin ganin an fitar da mutum miliyan 100 daga ƙangin talauci a cikin shekaru 10.

Ya ce an sake farfaɗo da shirin ne bayan jinkirin sama da shekaru 20 da shirin ya tsaya cak.

Da ya ke jawabi, Minista Adamu ya ce shirin zai samar da hekta 2,114 waɗanda za a riƙa tura masu ruwa daga madatsar ruwa ta Da Marke da ke Arewa maso Gabas da Ƙunshi ta cikin Jihar Kano.

Aikin noman rani da magudanan ruwa da ma-aikatar ruwa ta gudanar, sun shafi garuruwan Kazaure, Roni a Jihar Jigawa. Sai kuma Ƙunchi, Ɗambatta da Makoɗa cikin Jihar Kano.

Sarkin Kazaure Najib Adamu ya yaba wannan gagarimin shiri, kuma ya roƙi jama’a kada su bari wannan dama da su ka samu ta shiririce masu.