Ƴan Bindiga sun sace Sarkin Kajuru a Kaduna

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Kajuru ta Kaduna sun tabbatar da yin garkuwa da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13 a wani samame da suka kai gidansa daren jiya.

Sarkin mai shekaru 85 a duniya, an sace shi tare da matan sa uku, jikokin sa biyu da hadimansa uku da wasu mutun biyar.

Ɗaya daga cikin muƙarraban Sarkin wanda ya nemi a saƙaya sunansa ya tabbatar da harin.

An ruwaito cewa kwana ɗaya kafin faruwar lamarin, Sarkin ya ƙira taron tsaro; game da wani shiri na yin garkuwa da shi saidai daga dukkan alamu jami’an tsaro basu iya yin wani abu ba.

Masarautar Kajuru bai wuce nisan Kilomita 58 tazara da birnin Kaduna ba.