Ngige ya janye takarar shugaban ƙasa, ya zaɓi ci gaba da zama ministan Buhari

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya fasa takarar neman zama shugaban ƙasa da ya ke yi a ƙarƙashin APC, ya gwammace ci gaba da zama ministan Buhari.
Ngige ya fitar da sanarwar sa ta fasa fitowa takara a ranar Juma’a, sa’o’i kaɗan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zaman bankwana da Ngige, Akpabio da wasu ministoci takwas da za su sauka domin su nemi takarar muƙamai daban-daban.
Cikin sanarwar da Ngige ya fitar, ya ce ya sanar wa Shugaba Buhari canja ra’ayin da ministan yayi.
Sai dai kuma masu nazarin kurɗa-kurɗar na ganin cewa da wahala Buhari ya sake naɗa Ngige minista domin har ya rigaya ya yi bankwana da su.
Ngige ya kasance cikin mutum sama da 30 masu neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC da PDP.
Ya ce ya janye takarar sa, domin ya vi gaba da ayyukan alherin da ya ke wa al’ummar Najeriya.