Malami ya janye daga takarar gwamnan Kebbi duk da kurin da ya rika yi wai jama’a suka tilasta shi ya fito

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce ya janye daga takarar gwamnan Kebbi.
Hakan na kunshe ne a wata sako da ya aika wa Vanguard ranar Asabar.
Hakan na nuna cewa Malami ya zaɓi ya cigaba da za abisa kujerar minista da yake akai maimakon kurin da ya riƙa yi wai jama’a ne suka tilasta shi ya fito takara kuma yana yi don jama’a ne.
Kakakin Malami bai Umar Gwandu bai amsa kira da PREMIUM TIMES ta yi masa don samun karin bayani akan haka ba.
Minista Abubakar Malami na daga cikin ministoci shafaffu da mai ƴan gaba goshin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Malami na daga cikin ɗinbin jami’an gwamnati da suka sayi fom din takara a 2023. Malami na takarar ɗarewa kujerar gwamnan Kebbi idan wadin mulkin Abubakar Bagudu ya cika a 2023.
Sai dai kuma tun bayan umartar ministocin da suka sayi fom da Buhari ya yi na su ajiye mukaman su lissafin kowa ya canja.
Malami da sauran ministoci basu yi zaton Buhari zai ce musu su sauka tun yanzu ba.
Daga baya Malami, ya rubuta a shafin sa ta Tiwita cewa ya mika takardar ajiye aikin minista, sai kuma daga baya ya koma ya goge.
Masu yin sharhi akan siyasa na fanin Malami na cikin tsaka mai wuya gashi dai yana son kujerar gwamna wanda ake ganin zai iya yin nasara, amma kuma dole ya ajiye aikin minista tun yanzu shekara ɗaya kafin zabe.
Idan ba a manta ba ministan Shari’a, Malami ya yi kokarin majalisa ta amince da wata sabuwar doka da ya kirkiro na a rika bari ministoci na cigaba da zama a kujerun su har sai an kusa kammala mulki zaɓe ya kusa.
Sai dai wannan kudiri ta sa ba ta tsallake majalisar dattawa ba. Tuni suka wancakalar da ita suka ce ya saba wa irin dokar da ya kamata ya shiga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.