NESA TA ZO KUSA: INEC ta bayyana ranar zaben shugaban kasa a 2023

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 18 ga Fabrairu ne za a gudanar da Babban Zaben shekarar 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin jawabin da ya gabatar wajen taron dandalin sauraron jama’a a kan Kudirin KirKiro Dokar kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zabe ta Kasa wanda Kwamitin Hukumar Zabe na Majalisar Dattawa ya shirya a Abuja.

Farfesa Yakubu ya ce: “Wannan Hukuma ta Kosa ta san irin dokar da za ta yi aiki da ita wajen aiwatar da manyan zabubbukan shekarar 2023. A bisa ka’idojin da Hukumar ta kafa, za a gudanar da manyan zabubbukan 2023 ne a ranar Asabar, 18 ga Fabrairu, 2023, wanda ya kama shekara daya da wata tara da mako biyu da kwana shida daidai daga yau din nan ko kwanaki 660.”

Shugaban ya ce shekaru 13 bayan shawarar da Mai Shari’a Muhammadu Lawal Uwais ya bayar kan a kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zabe (National Electoral Offences Commission), da kuma wasu rahotannin kwamitoci daban-daban a kan batun, “a yau ga mu a wajen wannan taro na tarihi domin mu bada namu shawarwarin kan wannan doka.”

Ya ce, “Ba shakka, an dora wa INEC ayyuka masu yawa domin ana yin zabubbuka a sassan Nijeriya a duk tsawon shekara.

“Tun daga zaben 2015, an gudanar da shari’u 124 kan laifuffukan zabe amma a guda 60 kadai ne aka yanke hukunci.”

Ya Kara da cewa: “To amma, a yayin da mu ke jin dadi game da wannan taron na yau, mu na kuma so a fito da tsarin doka mai suna Dokar Zabe (Gyararriya) wanda a kan ta za a aiwatar da zabubbukan 2023, wanda za a yi a ranar 28 ga Fabrairu, 2023, kuma a rattaba hannu a kan ta a kan lokaci.”

Tun da fari, sai da Shugaban Kwamitin Hukumar Zabe na Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya bada tabbaci ga dukkan masu ruwa da tsaki cewa Kudirin Dokar Zabe (Gyararriya) na 2021 ya na samun kulawa kuma ana fatan Shugaban Kasa zai rattaba hannu a kan ta.

Gaya ya ce ba shakka kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zabe ta Kasa “zai canza labarin tsarin mu na gudanar da zabe.”

Wanda ya kawo Kudirin kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zabe ta Kasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce an fara Kudirin kafa hukumar ne tun a Majalisar Dattawa ta 8 lokacin da ya kawo shawarar Kudirin tare da Ovie Omo-Agege saboda sun fahimci cewa INEC ba ta iya hukunta ko da kashi 1 cikin dari na laifuffukan zabe, saboda haka akwai buKatar a dauke wannan aikin daga kafadun ta, a bar ta ta yi aikin ta da kyau.