‘Yan majalisa za su iya tsige Buhari idan babu abin da ya canja bayan Taron Dakile Matsalar Tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari zai iya fuskantar tsigewa daga Majallisar Tarayya matsawar aka ga babu wani abu da ya canja bayan Taron Dakile Matsalar Tsaro da aka shirya gudanarwa.

Dan Majalisar Tarayya Dachung Bagos, dan PDP daga Jihar Filato ne ya shaida haka, tare da cewa taron da majalisar za ta yi kan matsalar tsaro shi ne dama ta karshe da za su iya bai wa Shugaba Buhari.

Dachung Bagos ya yi wannan bayanin a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, a ranar Alhamis.

A ranar Laraba ce Majalisa ta kafa kwamitin musamman wanda Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ne shugaban kwamitin, wanda zai shirya taron musamman kan matsalar tsaron Najeriya.

An shirya za a gudanar da taron a ranakun 24 da 28 Ga Mayu.

Bagos ya ce idan taron ya kasa samar da wani kyakkyawan sakamakon magance matsalar tsaron da ta buwayi kasar nan baki daya, to fa majalisa ba ta da wni zabi sai dai kawai ta nemi Shugaba Buhari ya sauka kawai ya rufa wa kan sa asiri, ko kuma su tsige shi.

“Bayan wannan taro a za a yi, idan babu wani abin kirki dangane da magance matsalar tsaro, to bayan ‘yan watanni to za mu nemi Shugaba Buhari ya sauka. Saboda mu na da wannan karfin ikon na tsige Shugaban Kasa idan ya kasa tsare kasar da ya yi alkawarin tsarewa a lokacin da aka rantsar da shi.

“Saboda dai wannan taron shi ne dama ta karshe da uziri na karshe da za mu iya bai wa Shugaba Buhari. Mun san batutuwan da za mu tattauna a kai. Kuma mun san irin yadda ake bi mu na tuntubar mambobin majalisa dangane da wannan muhimmin batu.”

“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Majalisar Tarayya a wannan karo jaki za ta dirka wa duka, ba taiki ba. Za mu umarci ya sauka kawai, ko kuma mu tsige shi, idan Shugaban Kasa ya kasa kare rayukan jama’ar kasar nan.”

To sai dai ba a sani ba ko furucin Bagos na da goyon bayan ‘yan majalisar APC ko a’a.