Wasu Gwamnonin A Najeriya Sun Fi Dacewa Da Mulkin Soja, Daga Mustapha Soron Dinki

Mulkin siyasa idan babu farin ciki ya samu matsala. Amfanin siyasa shine ta samar da farin ciki mai girma a tsakanin mutane masu rinjaye.

Wannan ita ce cikakakykyiyar siffar gwamnatin siyasa. Kamar yadda wani masaninta mai suna John Stuat Mills yace.

Tun asali, mutane sun karbi tsarin dimokradiyya ne don su samu ‘yanci daga tsohon tsarin mulki na gargajiya. A dimokradiyyar gaske, gwamnati ta jama’a ce, wacce suka samar da ita da hannunsu don ta samar musu da cigaba. Saidai kuyanga tana haihuwar uwar gijiyarta a Najeriya.

A matsayinka na d’an siyasa, duk sanda ka saka takalmin qarfe, to daga ranar ba sunanka d’an siyasa ba saboda gwara ka saka kakin soja. Amma a dimokradiyya sunanka d’an kauye. Kuma ko da kafi kowa ilimi a Najeriya. Gaskiya ban san amfanin ‘yan majalisar jiha ba a wasu jihohin na Najeriya. Don duk lalacewar ‘yan majalisar tarayya a idon mutane sun fi na jihohi tasiri.

Gwamnoni sun mayar da ‘yan majalisar jiharsu kamar gayaunarsu. Misali, a jihar Kaduna, matakin korar mutane daga aiki a cikin yanayin rashin tsaro annoba ne. Jihar Kaduna tana cikin jihohin da suke fama da rashin tsaro a Najeriya.

Kuma kowa ya san cewa talauci yana sabbaba rashin tsaro sosai. Don dan Adam ba a so ya zauna bashi da abun yi, akwai matsala. Idan ba a inganta masa sana’a ba, bai dace a rushe tasa ba. Hatta zabtarewa maaikata albashi a jihohi irinsu Kano ba daidai bane. Balle kuma kora daga aiki.

Abinci shine bukatar dan Adam ta farko. Gina gari ba shine abunda yafi mahimmanci ba. An kori malaman makaranta a baya. Yanzu kuma ana kokarin korar ma’aikatan karamar hukuma dubu Ashirin. Mutane ake ginawa, su kuma sai su gina gari. Babu abunda yafi mutum mahimmanci a cikin kadarorin qasa. Allah ne yake halittar mutane, su kuma su gina alqaryarsu. Hatta Amerika, mutane ne suka ginata, karewa kenan. Yakamata gwamna ya sake tunani don ceto rayuwar al-umma.

Allah ya shiryar da mu.