JUYIN MULKIN NIJAR: Burkina Faso, Mali da Gini za su taya Nijar ragargazar kasashen da za su kai wa Nijar hari

A wani sabon rudani dangane da rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin sojoji a Nijar, kasashen Burkina Faso, Mali da Gini sun nuna goyon bayan su ga Nijar, tare da alkawarin za su taya Nijar ragargazar kasashen da za su kai wa Nijar hari
Burkina Faso da Mali sun fitar da sanarwar hadin guiwa a tsakanin su, cewa su na gargadin kada a kuskura a kai wa Nijar farmakin soja, domin duk wanda ya yi amfani da karfin sojoji a Nijar, to tamkar ya kai wa kasashen biyu ne hari.
Sun ce amfani da karfin soja a Nijar zai iya ragargaza yankin Afrika ta Yamma baki dayan sa.
Kasashen biyu sun karanta wannan gargadin a gidajen radiyo da talbijin na kasashen biyu, kwana daya bayan Kungiyar ECOWAS ta yi gargadin yin amfani da karfin soja kan gwamnatin mulkin soja ta Nijar, wadda ta kwace mulki a hannun gwamnatin Mohammed Bazoum.
Sannan kuma sun bayyana cewa duk wani takunkumi da za a kakaba wa Nijar, to rashin adalci ce, rashin tausayin al’umma ne, kuma rashin kunya ce.
Ita ma kasar Gini ta yi sanarwar nuna goyon baya ga gwamnatin mulkin soja ta Nijar. Sanarwar ta ja hankalin kasashen Afrika ta Yamma da su karfafa dankon dangantakar ‘yan’uwantakar da ke a tsakanin su.
Haka dai Shugaban Mulkin Sojan Gini, Kanar Mamadi Doumbouya ya bayyana a cikin sanarwar.
Haka kuma Gini ta ce za ta taimaka wa Nijar ta kowace hanyar da ta dace, tare da tsame kan ta daga kokarin kakaba wa Nijar takunkumi da ECOWAS ke shirin yi.
Yanzu dai Nijar na karkashin Janar Abdourahamane Tchiani, tsohon Shugaban Dakarun Tsaron Fadar Shugaban Kasa.
Ya ce sun hambarar da Bazoum ne saboda rashin iya yin wani katabus a fannin matsalar tsaro da barazanar ‘yan Boko Haram bangaren Al-kaida da ISIS a Nijar.
A wata sabuwa kuma, tuni sojojin Nijar masu rike da gwwamnati sun fara damke hambararrun masu rike da gwamnatin da suka hambaras.
Sun kama Ministan Ma’adinai, Ministan Harkokin Man Fetur, Ministan Harkokin Cikin Gida, Ministan Sufuri da Ministan Tsaro.
Haka kuma sun damke tsohon shuggaban jam’iyya mai mulki wadda suka hambaras, wato PNDS.