NA CIKA ALKAWARIN DA NA ƊAUKA WA ƳAN NAJERIYA: Jirgin Nigeria Air zai fara tashi cikin Disamba – Buhari

Yayin da talakawa a faɗin ƙasar nan ke fama da ƙuncin rayuwa da tsadar abinci da kuma rashin tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƙoƙarin kafa kamfanin Nigeria Air an kusa kammalashi da kashi 91 bisa 100.
Buhari ya ce ana kayutata zaton ƙaddamar da shi a cikin watan Disamba, kafin ƙarshen wannan shekarar.
Buhari ya sha wannan alwashin a Taron Bin Diddigin Ayyukan Ministoci na 3 da aka shirya a ranar Litinin, a Abuja.
Ya bayyana cewa kamfanin Zirga-zirgar Jiragen zai fara amfani da tashoshin Legas da Abuja ne, wanda Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya ta amince da su.
Ya ce nan ba da daɗewa ba kuma za a tantance filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal domin a ba su satifiket na amincewa da su.
Nigeria Air dai ya lashe naira bilyan 14.6, kuma su ne karon hannun jarin Najeriya na kashi 5 ɗin ta a cikin kamfanin.
Tattalin Arzikin Najeriya Ya Yi Tashin Gwauron Zabo -Buhari:
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan tattalin arzikin Najeriya, wanda ya ce sau bakwai kenan a jere ma’aunin sikeli na nuna cewa ya bunƙasa, tun bayan gararin da ya shiga a cikin 2020.
“Yawancin ɓangarorin tattalin arzikin ƙasa sun bunƙasa ne albarkacin tsare-tsaren da wannan gwamnatin ta bijiro da su masu kawo ci gaba,” inji Buhari.
Tattalin Arzikin Fasahar Sadarwar Zanmmani ya samu gagarimin ci gaba -Buhari:
Buhari ya ce an samu gagarumin ci gaba a Ma’aikatar Bunƙasa Tattalin Arzikin Fasahar Sadarwar Zamani, wato Digital Economy.
Ya ce ɓullo da ƙarfin sadarwar zamani ta ƙarfin zangon data ta 4G ya haifar da kafa tashoshin 4G har guda 36,751 a faɗin ƙasar nan.”
Buhari ya ce miƙa wa ‘yan kasuwa harkar wutar lantarki ya kawo nasarar samun hasken lantarki ga yankunan da ke fama da ƙarancin wutar lantarki da masana’antu da dama.
Ya yi maganar cewa har yanzu burin Gwamnatin Tarayya na samar da ƙarfin wuta miga 25,000 cikin shekaru shida ya na nan, domin Gwamnatin Tarayya ta yi haɗin guiwa da kamfanin Siemens na Jamus domin tabbatar da hakan.”
Ya ce tuni ma tiransifomi zubin farko duk sun iso Najeriya.
“Rundunar Sojojin Saman Najeriya ya sayo jiragen yaƙi 38, kuma wasu ana sa ran isowar wasu 36. Sai kuma su ma Sojojin Ruwa an samar masu da jiragen ruwa na yaƙi.
Najeriya Ta Kara Ɗaukar ‘Yan Sanda 20,000 -Buhari:
Shugaba Buhari ya ce an ɗauki waɗannan ‘yan sanda tare da horas da su a cikin 2020 da 2022.