Akwai akalla katin zaɓe 13,442 da ba a karba ba a jihar Borno – INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar cewa akwai katin zaɓe 13,442 da masu su basu karba ba a jihar Borno.
Shugaban sashen wayar da kan mutane kan harkokin zaɓe na INEC Shuaibu Ibrahim ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Maiduguri.
Ibrahim ya ce INEC ta yi wa mutum 25,171 rajistar katin zaɓe a bana a jihar inda daga ciki kati 11,729 ne kadai masu su suka karba.
Ya ce bana hukumar ta yi wa mutum 25,822 canjin rumfar zabe da kuma canjin kati inda daga ciki mutum 4336 na masu bukatar canjin wuri suka karbi katinsu sannan mutum 1,684 na masu bukatar canjin kati suka karbi katin su.
Ibrahim ya ce INEC ta ci gaba da wayar da kan mutanen mahimmancin karban katin zaɓeganin cewa akwai katin zaɓe 167,209 na mutane dake dankare a hukumar ba a zo an karbe su ba.
INEC ta ce hukumar ta yi wa mutum 248,241 rajistar katin zaɓe kafin aka rufeyin rajistar.