Ƴan sanda sun kama Abubakar da ya kashe mahaifinsa don ya mallakin dukiyar uban wato ya ci gado

Rundunar Ƴan sandan jihar Neja ta kama wani matashi mai suna Abubakar Mohammed-Buba wanda ya kashe mahaifinsa Alhaji Mohammed Buba mai shekara 52 domin ya ci gadonsa.

Kakakin rundunar ƴannsandan Wasiu Abiodun ya ce rundunar ta kama Mohammed-Buba wanda bai wuci shekaru 20 ba ranar 29 ga Disamba 2021 a Chanchaga dake cikin garin Minna.

Abiodun ya ce an kama Mohammed-Buba a lokacin da ya je siyar da daya daga cikin kadarorin mahaifinsa.

“Mohammed-Buba ya shaida wa jami’an tsaron cewa shine ya aika da wani domin ya kashe mahaifinsa saboda dukiyar uban ta zamo nashi.

“Mohammed ya ce ya hada baki da Wani abokinsa Aliyu Mohammed suka baiwa wani Ɗan iska kwangilar kashe mahaifinsa akan kuɗi naira 100,000 da naira 10.

Ya ce ya biya wannan ɗan iskan naira 50,000 lakadan. Ƴan sanda sun kama shi a lokacin da ya je siyar da wani kadarar mahaifinsa domin ya cika wa wanda ya ba kwangilar kashe mahaifin sa kuɗin da ya rage wato naira 50,000 da naira 10 kenan.

Abiodun ya ce rundunar ta kama Abubakar inda ya nuna musu inda suka jefar da gawar majaifin sa Alhaji Mohammed Buba.

Ya ce an kashe Mohammed Buba ranar 13 ga Oktoba 2021 a gidan sa dake Korokpan a karamar hukumar Paikor.

Abiodun ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka ne za ta ci gaba da gudanar da bincike sannan za a kai Abubakar kotu bayan ta kammala.