Muhawara Kan Bashin Naira Tiriliyan 71 Da Ake Bin Gwamnatin Najeriya

Watanni shida da cikar wa’adin mulkin shugaba Mohammadu Buhari, bincike ya nuna cewa jimlar basussuka da gwamnatin Tarayya ta ciwo da sauran lamuni da ta yi sun kai Naira triliyan 71.5 amma masana tattalin arziki sun bayyana ra’ayi mabanbanta akan haka.