Gasar Cin Kofin Duniya: Kamaru Ta Sha Ci Daya Mai Ban Haushi A Hannun Switzerland A Qatar
Breel Embolo ne ya zura kwallo a ragar kasar haihuwarsa da ya baiwa Switzerland nasara da ci 1-0 a kan Kamaru a gasar cin kofin duniya da suka fafata a rukunin G a filin wasa na Al Janoub a yau Alhamis.