Messi Na Atisaye Yayin Da Suke Shirin Wasansu Na Gaba Bayan Kunen Doki Da Chile

A shirye muke mu kara, za kuma mu ci gaba da fafatawa don mu lashe dukkan wasanninmu, gaba dai Argentina” Messi ya rubuta a shafinsa na sada zumunta hade da hotonsa da ke nuna lokacin da zai buga kwallon da ya ci wacce ta ba su damar yin kunnen doki da ci 1-1 da Chile.