Na baku umarnin shiga daji ku farauto mana ƴan bindiga~ Gwamnan Kebbi da Ƴan Sa Kai

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya karbi bakwancin ƙungiyar Ƴan Sa Kai (Vigilantes) da na Mafarauta a gidan gwamnatin jihar dake Birnin Kebbi.

Ƙungiyiyin sun ziyar gwamnan ne domin yi masa jajen abin da ya faru na sace ɗaliban FGC Birnin Yauri, kuma suka samu tarba daga Gwamnan tare da takwarorinsa na jihohin Jigawa Muhammad Abubakar Badaru da na jihar Ekiti wanda shine shugaban Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi.

A yayin jawabinsa, Gwamna Abubakar Bagudu ya jinjinawa ƙungoyin biyu bisa aiyyukan taimakawa jami’an tsaro da suke yi a faɗin jihar.

Ya baiwa Mafarauta da Ƴan Sakai tabbacin yin magana da hukumomin tsaro domin samun cikakken ikon shiga dazuka domin farautar ƴan bindiga da ke neman maida jihar mafakar su.

A cewarsa” Ina umartan ku da ku koma gida ku cewa kowa na ƙira gayya. Zan yi magana da shuwagabannin tsaro kuma za mu faɗawa ƴan ta’addan nan cewa mu haɗu daji.”

Da yake nashi jawabi a madadin Gwamnonin Najeriya, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi, ya yaba da kokarin ƙungiyoyin Mafarautan da na Ƴan Sa Kai.

Yana mai cewa, “Za mu ɗauki darasi daga abin da muka ga ya faru a nan muma mu yi irin haka a jihohin mu”.