MATSALAR RASHIN TSARO: An kafa kwamitin dalilin salwantar bindigogi 178,459 a hannun ‘yan sanda

Majalisar Tarayya ta kafa kwamitin da zai binciki dalilan salwantar bindigogi har 178, 459 a hannun ‘yan sandan Najeriya.

Wannan binciken dai ya taso ne bayan da Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya, ya aika wa Majalisa da rashoton binciken 2019.

A cikin rahoton, Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya, Adolptus Aghughu ya bayyana cewa aƙalla bindigogi 178,459 sun salwanta a hannun ‘yan sandan Najeriya, kuma jami’an tsaro ba su bada bayanan yadda aka yi da bincigogin ba.

Ya ce akwai samfurin AK 47 masu ɗimbin yawa, da fistol da rafil da tulin albarusai da sauran nau’o’in makamai, duk sun salwanta.

Amincewa a yi binciken dai ya samu karɓuwa ne bayan da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Toby Okechukwu ya tayar da batun, a bisa hujjar sa ta rahoton Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya.

Toby ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda ‘yan sanda ba su ajiye rekod na dukkan bayanan salwantar makaman su.

Ya bada misali da Babban Barikin Mobal na PMF Squadron da ke Abuja, rahoton da ‘yan sanda su ka bayar ya sha bamban da rahoton Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗe, kuma aka tabbatar da salwantar bindigogi har 46 tsakanin shekarar 2000 zuwa Fabrairu 2019.

Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase, ya ce babu buƙatar sake kafa wani kwamiti. “Tunda akwai kwamitin makamai na majalisa, a bar shi ya yi binciken.

Kwamitin Binciken na ƙarƙashin shugabancin Abubakar Falala, Ɗan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa.