Har yau babu takamaiman matsayar gwamnati kan tallafin fetur -Majalisar Zartaswa

Kwana ɗaya bayan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kuskura ta janye tallafin fetur, talakawa za su shiga masifar da ta fi ta yanzu ƙunci, Majalisar Zartaswa ta fito ta ce har yau Gwamnatin Tarayya ba ta cimma matsaya ba a kan batun cire tallafin fetur ko kada a cire shi.

Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a ranar Alhamis.

A taron wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya shugabanta tare da Gwamnonin Najeriya, ya ce har yanzu ana tattaunawa kan makomar batun janye tallafin man fetur, amma ba a cimma matsaya ba tukunna.

“Idan kun tuna ai an kafa wani kwamiti ƙarƙashin Gwamna Nasiru El-Rufai, kan batun tallafin mai, wanda a nan Najeriya ake sayar da lita ɗaya ta fetur naira 162, amma a sauran ƙasashe maƙwautan mu farashin ya nunka.

“A shekarar da ta gabata an kashe kusan naira tiriliyan biyu wajen cike gurbin kuɗaɗen tallafin fetur. Waɗannan maƙudan kuɗaɗe kuwa za a iya gina manyan titina da su, a inganta ilmi kuma a bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya.

“To a kan haka ne har yanzu ake ci gaba da tattauna shin za a ci gaba da kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗen da ya kamata a yi wa talaka aiki, sai a kashe su ga masu motoci kaɗai don samar musu fetur a sauƙaƙe”

Buhari Bai Taɓa Shaida Wa Kowa Kewa Za A Cire Tallafin Mai Ba -Sanata Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa a yanzu dai ba za a cire talalfin man fetur ba, kamar yadda jaridu da soshiyal midiya su ka riƙa yayatawa.

Lawal ya bayyana haka a ranar Talata da dare, ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawa a keɓance da Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar yadda Lawan ya bayyana masu, ya ce Buhari ya ce masa bai sanar da kowa cewa zai cire tallafin mai kamar yadda aka riƙa yayatawa ba.

“Na tattauna da Shugaban Ƙasa kan batutuwa da dama, ciki har da batun masu tayar da ƙayar baya a wasu sassan ƙasar nan.

“Jama’a da dama na nuna damuwar su kan batun cire tallafin fetur. To a matsayin mu na wakilan jama’a, dole mu ma wannan batu ke damun mu.

“Na samu Shugaban Ƙasa kuma ya sanar da ni cewa bai sanar da kowa cewa zai cire tallafin fetur ba.”