Cire tallafin mai zai ƙara ruruta wutar matsalolin da ‘yan Najeriya ke fama da su -Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar ya ja kunnen Gwamnatin Tarayya cewa a kul idan ta janye tallafin fetur, har man fetur ya ƙasa tsada, to za a ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin bala’in da ya fi wanda su ke ciki a yanzu.

Abubakar ya yi jawabin ne a wurin Taron Shekara-shekara na Daily Trust, taro na 19 da aka gudanar a ranar 19 Ga Janairu, a Abuja

Sunan taken taron dai shi ne “Zaɓen 2023: Siyasa, Tattalin Arziki Da Rashin Tsaro.”

A cikin watan Nuwamba ne dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta cire tallafin mai a cikin 2022.

Dama kuma ko ba ta ba ta faɗa ba, tuni akwai batun a cikin Sabuwar Dokar Fetur ta 2021, wadda ba a daɗe ba Shugaba Buhari ya sa mata hannu cikin watan Oktoba.

Kamfanin NNPC ya sanar ta hannun Shugaban Kamfanin, Mele Kyari cewa litar fetur za ta iya kai naira 460 idan aka cire tallafin fetur.

Ita kan ta gwamnatin tarayya ta bakin Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed, ta ce gwamnati za ta raba wa marasa galihu mutum miliyan 40 kowane naira 5,000 har tsawon watanni shida, idan aka cire tallafin, domin su rage raɗaɗin zafin ƙuncin rayuwa.

Abdulsalami wanda shi ne shugaban taron, ya gargaɗi gwamnati ta rufe shafin ƙarin kuɗin mai, saboda bala’in da talakawa ke ciki na matsalolin rashin tsaro, ƙuncin rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki, wanda ya nunka farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi.

“Matsalar tsaro a ƙasar nan ta ƙara muni kuma ta ƙara kassara tattalin arziki. Ga rashin aikin yi. Sama da majiya ƙarfi miliyan 18 a ƙasar nan na fama da tantangaryar takaucin da ya afka masu kuma ya yi masu ɗaurin-gwarmai. To duk waɗannan sun ƙara ruruta matsalar tsaro.

“Kai a yanzu Najeriya na fama da ƙazamar matsalar tsaron da ɓarkewar korona ta haifar da kuma mummunar fitinar ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya.

“Ku dubi yadda farashin abinci ke ƙara tashi a kullum, ya na ci gaba da wuce ƙarfin aljihun talaka. A kan haka kuma wai talaka na jiran tsammanin tashin farashin man fetur nan da watanni masu zuwa. Duk mun san cewa idan aka yi haka, to miliyoyin ‘yan Najeriya za su afka cikin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziki.” Inji Abdulsalami.

Babban Baƙo mai jawabi Gwamnan Jihar Barno, ya danganta salsalar matsalolin da ake fama da su ga wasu gwamnonin da ba su maida hankali wajen bunƙasa ilmi da samar da kayan more rayuwa ba a yankunan karkara.

Ya ce su da manyan ma’aikatu sun riƙa karkatar da ɗimbin kuɗaɗen da har duniya ta naɗe ba za su iya kashewa ba, kuma ba su amfana wa jama’a da kuɗaɗen ba.

Ya ce ya kamata a zaɓi shuagabanni bisa cancanta kawai ko ma daga wane ɓangaren yanki ko addini ne za su fito.

Sauran waɗanda su ka yi yawabai sun haɗa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar, wanda ya ce mu na matuƙar buƙatar mutanen kirki, na ƙwarai kuma masu nagarta a cikin siyasa.

Sauran manyan baƙi a wurin har da Tsohon Maitaimakin Shuagan Ƙasa, Atiku Abubakar.