MATSALAR MAI TA KARYA FUKAFUKIN JIRAGE: Man da ke gare mu bai wuce na zirga-zirgar kwana uku ba -Masu kamfanonin jiragen sama

Masu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya sun bayyana cewa wadataccen man da su ke da shi a ƙasa bai wuce ya kai su yin zirga-zirga da jigilar kwanaki uku kacal ba.
Sun bayyana cewa lamarin samun mai ya taɓarɓare ne saboda tsada da ƙarancin da ya yi.
Shugaban Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Air Peace, kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masu Jiragen Sama na Najeriya, Allen Onyema ne ya bayyana haka a wurin zaman saurare a gaban Kwamitin Binikinen Matsalar Man Jiragen Sama na Majalisar Tarayya.
Onyema ya ce ba mamaki kamfanonin jirage su fara cajin naira 120,000 a matsayin kuɗin tikitin shiga jirgi a cikin Najeriya.
Ya ce “idan farashin tikitin jirgin sama a cikin Najeriya bai kai Naira 120,000 ba nan da kwanaki uku, to zirga-zirgar ma ba za ta yiwu ba. Kuma nan da kwanaki uku ɗin ma za mu ajiye jiragen, mu daina tashi.”
Ya yi ƙorafin cewa masu sayar masu da mai sun ƙara kuɗi, amma sun ƙi sanar da su yadda su man ke kamawa a wurin su.
Onyema ya ce matsawar masu sayar da man jirgi ba su rage farashin lita ɗaya daga naira 670 da ake sayar wa masu kamfanonin jiragen sama ba, to ya kamata hukuma ta bai wa masu kamfanin jiragen sama lasisin shigo da mai kawai.
“Mu roƙon da mu ke wa Gwamnatin Tarayya shi ne a ba mu lasisin shigo da man jiragen mu. Saboda mu a nan Najeriya, abin da wasu ƙasashen ke kashewa su yi wa jirgi uku inshora, a Najeriya jirgi ɗaya kaɗai mu ke iya yi wa inshora da kuɗaɗen. Kun ga kenan harkokin zirga-zirgar jiragen sama a ƙasar matacciya ce akwai.” Inji Onyema, mai Air Peace.
Mai Ya Kashe Bakin Tsanya: ‘Za Mu Rufe Dukkan Gidajen Radiyo Da Talabijin Na Arewa’ -Masu Kafafen Yaɗa Labarai:
Ƙungiyar Masu Gidajen Radiyo da Talabijin na Arewa (NBMOA), sun koka dangane da matsalar ƙaranci da tsadar fetur, baƙin mai da gas, har ta kai ga sun yi barazanar cewa nan ba da daɗewa ba za su rufe gidajen radiyo da talabijin na arewacin Najeriya.
Kungiyar ta ce ƙarin matsalar kuma ta haɗa da gagarimar matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita, wadda ta ƙara dagula lissafin gudanar da ayyuka baki ɗaya.
Wannan ƙungiya dai ta ƙunshi dukkan masu gidajen rediyo da talabijin masu zaman kan su da ke Arewa.
Yayin da ake fama da matsalar fetur, Babban Manajan Watsa Labarai na NNPC, Garba Deen Muhammad a kwanan baya ya ce an raba mai sosai, amma jama’a su ƙara haƙuri, domin akwai mai wadatacce.
NNPC ta umarci masu masu deffo su riƙa lodin mai ba dare ba rana domin a cike giɓin ƙarancin sa.
Muna Cikin Matsanancin Halin Ƙunci -Masu Gidajen Radiyo da Talabijin:
A wata hira da Shugaban Ƙungiyar Masu Gidajen Radiyo da Talabijin na Arewa, Tijjani Ramalan ya yi da BBC Hausa a ranar Litinin, ya ce kafafen watsa labaran su na shan wahala sosai wajen gudanar da ayyukan su, saboda matsanancin wahalar fetur da gas da baƙin mai.
“Mu na shan wahala sosai kafin a riƙa jin labarai da shirye-shiryen mu a kullum, saboda na farko dai babu wutar lantarkin da za mu iya dogaro da ita, gas shi ma ya yi tsada kuma ya na karanci. Abin takaici ne ƙwarai, saboda babu wata mafita daga wannan karankatakaliya.
“Ya kamata Ku sani cewa gaba ɗayan ayyukan mu na tafiya ne ta hanyar kunna janareto domin mu samu wuta, saboda babu wutar lantarki kwata-kwata.” Inji shi.
Ramalan wanda shi ne Shugaban Gidan Talabijin da Liberty Radiyo, ya ce a yanzu mai injin janareto ya kai Naira 730 duk lita 1, abin da ya ce a gaskiya ba za su iya ci gaba da sayen sa a haka ba.
Ramalan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gyara matsalar wutar lantarki.
Kuma ya ƙara kokawa a kan matsalar tsada da ƙarancin mai.