GAGARIMAR MATSALAR MAI: ‘Za mu rufe dukkan gidajen radiyo da talabijin na Arewa’ -Masu kafafen yaɗa labarai

Ƙungiyar Masu Gidajen Radiyo da Talabijin na Arewa (NBMOA), sun koka dangane da matsalar ƙaranci da tsadar fetur, baƙin mai da gas, har ta kai ga sun yi barazanar cewa nan ba da daɗewa ba za su rufe gidajen radiyo da talabijin na arewacin Najeriya.
Kungiyar ta ce ƙarin matsalar kuma ta haɗa da gagarimar matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita, wadda ta ƙara dagula lissafin gudanar da ayyuka baki ɗaya.
Wannan ƙungiya dai ta ƙunshi dukkan masu gidajen rediyo da talabijin masu zaman kan su da ke Arewa.
Yayin da ake fama da matsalar fetur, Babban Manajan Watsa Labarai na NNPC, Garba Deen Muhammad a kwanan baya ya ce an raba mai sosai, amma jama’a su ƙara haƙuri, domin akwai mai wadatacce.
NNPC ta umarci masu masu deffo su riƙa lodin mai ba dare ba rana domin a cike giɓin ƙarancin sa.
Muna Cikin Matsanancin Halin Ƙunci -Masu Gidajen Radiyo da Talabijin:
A wata hira da Shugaban Ƙungiyar Masu Gidajen Radiyo da Talabijin na Arewa, Tijjani Ramalan ya yi da BBC Hausa a ranar Litinin, ya ce kafafen watsa labaran su na shan wahala sosai wajen gudanar da ayyukan su, saboda matsanancin wahalar fetur da gas da baƙin mai.
“Mu na shan wahala sosai kafin a riƙa jin labarai da shirye-shiryen mu a kullum, saboda na farko dai babu wutar lantarkin da za mu iya dogaro da ita, gas shi ma ya yi tsada kuma ya na karanci. Abin takaici ne ƙwarai, saboda babu wata mafita daga wannan karankatakaliya.
“Ya kamata Ku sani cewa gaba ɗayan ayyukan mu na tafiya ne ta hanyar kunna janareto domin mu samu wuta, saboda babu wutar lantarki kwata-kwata.” Inji shi.
Ramalan wanda shi ne Shugaban Gidan Talabijin da Liberty Radiyo, ya ce a yanzu mai injin janareto ya kai Naira 730 duk lita 1, abin da ya ce a gaskiya ba za su iya ci gaba da sayen sa a haka ba.
Ramalan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gyara matsalar wutar lantarki.
Kuma ya ƙara kokawa a kan matsalar tsada da ƙarancin mai.