Matawalle ya naɗa sabon shugaban hukumar ZAROTA

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Mai girma Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya amince da naɗin Kanal Rabi’u Garba Ɗan Dokaji a matsayin sabon shugaban hukumar kula da cinkoson ababen hawa ta jihar (ZAROTA).

Naɗin ya biyo bayan dakatar da aiyukan hukumar wanda gwamnan ya yi a ranar Alhamis bayan rikici da ya kaure tsakanin jami’an ZAROTA da direbobin manyan motoci.

Tuni dai gwamnan ya sa a binciki ainahin abin da ya janyo rikivin na safiyar yau da ya janyo cinkoso a birnin Gusau bisa rufe babban mashiga da fita fadar jihar.