Najeriya za ta karbi karin kwalaben maganin rigakafin Korona miliyan 3.92 daga COVAX

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta karbi karin kwalaben maganin rigakafin Korona na Oxford-AstraZeneca daga asusun COVAX.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka ranar Talata a Abuja.

Shu’aib ya ce Najeriya na sa ran karban kwalaben maganin a karshen watan Yuni ko kuma a watan Agusta.

Idan ba a manta ba a ranar 5 ga Maris ne aka fara yi wa mutane allurar rigakafin korona a kasar nan bayan an karbi kwalaben maganin rigakafin guda miliyan 4 daga hannun asusun COVAX.

A ranar 21 ga Maris kamfanin MTN ta bai wa gwamnati gudunmawar kwalabe 300,000 sannan a ranar 6 ga Afrilu kasar India ta bai wa gwamnati kwalaben maganin rigakafin guda 100,000.

Jimlar adadin yawan kwalaben maganin rigakafin korona da Najeriya ta samu a lokacin ya kai miliyan 4.4.

A dalilin karancin maganin rigakafin gwamnati ta sa a dakatar da yi wa mutane allurar rigakafin domin a samu wanda za a yi wa mutane karo na biyu.

Allurar rigakafin korona a Najeriya

Hukumar NPHCDA ta bayyana cewa mutum 1,978,808 ne suka bada kansu domin allurar rigakafin korona zangon farko a kasar nan.

Sannan a zango na biyu mutum 680,345 suka yi allurar rigakafin korona a kasar nan.

Shu’aib ya yi kira ga wadanda suka yi allurar rigakafin korona zangon farko da su gaggauta zuwa domin yin allurar zango na biyu.

Ya ce gwamnati ta kara yawan wuraren ta ake yin allurar a dalilin haka za a samu canjin wurin yin allurar rigakafin.

Zuwa yanzu mutum 167,078 ne suka kamu da cutar sannan mutum 2.117 sun mutu.

Za a ci gaba da yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na farko.

Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati ta ci gaba da yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na farko a kasar nan.

Ya ce tun dama can a ranar 24 ga Mayu gwamnati ta dakatar da yi wa mutane allurar rigakafin korona saboda karancin maganin da ake fama da shi a kasan.

“Tun bayan da aka dakatar da yi allurar rigakafin ne mutane suka matu a ci gaba da yin allurar rigakafin.

Shu’aib ya ce duk wadanda suka dara shekaru 18 za su iya bada kansu domin yin allurar rigakafin sannan za su iya dawowa domin yin allurar zango na biyu bayan sati 6 zuwa 12.

Ya ce sakamakon binciken da hukumar gudanar da bincike na kasar Amurka PHE ta gudanar ya nuna cewa maganin rigakafin korona na Oxford-Astrazeneca na da ingancin kashe sabuwan nau’in cutar korona B.1.617.2 dake kisan mutane a kasar India.

Shu’aib ya ce gabatar da wannan sakamako ya karfafa gwiwowin gwamnati wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.