Mataimakin Gwamnan Kebbi ya rasa babban ɗansa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Sama’ila Yombe Dabai ya rasa babban ɗansa.

A wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin gwamnan kan harkokin sadarwa Atom Turba Ishaku ya fitar, Alhaji Ibrahim Sama’ila Yombe ya rasu a yau Lahadi a birnin Karthoum na ƙasar Sudan bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar ta ce za a sanar da lokacin da za a yi masa Sallar Jana’iza bayan an kammala kimtsawa bisa koyarwar addinin musulunci.