DA ƊUMI-ƊUMI: An rushe shuwagabannin jam’iyyar a jihar Zamfara

Kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar APC a matakin ƙasa ya rusa shugabannin jam’iyyar a jihar Zamfara.

Sakataren jam’iyyar na ƙasa a matakin riƙon ƙwarya, John Akpanuodedehe ne ya sanar da rushewar a wata wasiƙa mai kwanan wata 9 ga watan Yulin, 2021 kuma ya aike wa shugaban jam’iyyar na riƙo a jihar, Lawal Liman.

Kamfanin Dillancin Labaran (NAN) ya ce rusawar ta fara aiki nan take.

Ya ci gaba da cewa an kafa kwamiti riƙon ƙwarya wanda zai tafiyar da al’amuran jam’iyyar a jihar mai ɗauke da mutum uku.

An naɗa Hassan Mohammed a matsayin shugaban kwamitin tare da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Muntari Anka a matsayin mataimakin shugaba yayin da Abdullahi Shinkafi, tsohon sakataren gwamnatin jihar, zai yi aiki a matsayin Magatakarda.

Kwamitin riƙon ƙwaryar jam’iyyar ta ƙasa ta miƙa godiyarta ga wadanda aka sallama sannan ta buƙace su da su ba da goyon baya ga sabon shugabancin jam’iyyar a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa rushe shuwagabannin ya biyo bayan sauya sheƙar Gwamnan jihar ta Zamfara Muhammad Bello Matawalle daga PDP zuwa APC.

An kuma ayyana Gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar kamar yadda yake a cikin ƙundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.