Tsohon mataimakin Gwamnan Kaduna Bantex ya rasu

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni daga gidan gwamnatin jihar Kaduna na bayyana rasuwan tsohon Mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bala Bantex.

Majiyar HAUSA DILY TIMES daga gidan gwamnatin Kaduna ta tabbatar da labarin mutuwar.

A cewar majiyar, Barnabas Bala Bantex ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 64 a duniya.

Bantex ya kasance Mataimakin Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i a wa’adin gwamnatinsa na farko daga 2015 zuwa 2019 inda ya tsaya takaran Sanatan Kaduna ta Kudu.