Masarautar Ƙaraye ta dakatar da dagacen da ya saida wa Fulani fili suka gina masallaci

A masarautar Karaye dake jihar Kano ta dakatar da dagacen kauyen Butu-Butu dake karamar hukumar Rimingado, Abdullahi Sa’adu a dalilin saida wa wasu Fulani makiyaya a fili a kauyen.

Kakakin masarautar Karaye Haruna Gunduwawa ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a.

Gunduwawa ya ce siyar da fili da Sa’adu ya yi wa Fulani makiyaya ya haddasa rikici tsakanin Fulanin da jama’an gari.

Ya ce rikicin ya dauko asali tun bayan saida wa fulani makiyaya filin sannan da gina masallaci da suka yi bisa filin ba tare da samun amincewar hukuma da na gaba da shi ba.

An kuma gano cewa sun gina wannan masallaci ba tare da bi doka ba.

Gunduwawa ya ce an dakatar da Sa’adu ne domin kwamitin da aka kafa ta gudanar da bincike akan lamarin.

Kwanakin baya Magajin Rafin Karaye Auwalu Tukur da sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II sun ja wa Sa’adu kunne ta kan wasu laiffuka da ya rika aikata wa.
Tuni har an nada Habibu Madakin Shamaki ya kula da masarautar har sai an kammala bincike.