2023: Kirista ne ya fi dacewa ya shugabanci kasar nan a 2023 – Kiran Kungiyar NEG

Kungiyar ‘Nigeria Equity Group (NEG)’ ta bayyana cewa kamata ya yi Najeriya ta samu shugaban ƙasa daga yankin Kudancin kasar nan kuma Kirista a shekarar 2023.

Kungiyar ta ce tana goyan bayan shawarar da kungiyar gwamnonin Kudu suka yi cewa a 2023 dan kudu ne ya fi cancanta ya mulki Najeriya kuma Kirista.

Kungiyar ta bayyana haka ne a taron manema labarai da ta yi a cikin wannan mako a Abuja.

Shugaban kungiyar Emeka Nwosu ya ce idan har ana so a yi wa yankin Kudancin kasar nan adalci to lallai a tabbata wanda zai shugabanci Najeriya dan kudu ne kuma cikakken kirista.

Nwosu ya ce yin haka shine zai baiwa wasu yankunan kasarnan daman dana shugabancin kasar nan sannan ya kawar da zaman doya da manja da ke tsakanin mabiya addinai biyun kasar nan, wato, kiristoci da musulmai.

“Idan ba a manta ba tun da gwamnatin farin hula ya dawo a shekarar 1999 shugabancin kasar nan ana yin tsarin karba-karba ne tsakanin musulmai da kirsta wanda yanzu shekara 22 kenan. Amma idan shugabancin ya kara komawa hannun musulmi a 2023 za a yi wa kiristocin kasar nan rashin adalci kenan.

“Bai dace a hana kiristoci shugabancin kasar nan ba domin yawan su ya kai rabin yawan mutanen Najeriya.